Daga Dapchi zuwa Chibok: Sabuwar Wasikar Reno Omokri ga Lai Mohammed

Daga Dapchi zuwa Chibok: Sabuwar Wasikar Reno Omokri ga Lai Mohammed

Hankalina ya dauku a kan bayanan da naji na daga Ministan Watsa Labaru, Alh. Lai Mohammed, ya yi, ya nuna cewa gwamnatin Jonathan bata yi komai ba lokacin da aka sace 'yan Matan Chibok ba, amma gwamnatin Buhari tana aiki tukuru da aka sace 'Yan Matan Dapchi.

Daga Dapchi zuwa Chibok: Sabuwar Wasikar Reno Omokri ga Lai Mohammed

Daga Dapchi zuwa Chibok: Sabuwar Wasikar Reno Omokri ga Lai Mohammed

Hankalina ya dauku a kan bayanan da naji na daga Ministan Watsa Labaru, Alh. Lai Mohammed, yayi, ya nuna cewa gwamnatin Jonathan bata yi komai ba lokacin da aka sace 'yan Matan Chibok ba, amma gwamnatin Buhari tana aiki tukuru da aka sace 'Yan Matan Dapchi.

Lokacin da yake jawabi alokacin bude bikin shirye-shirye na Editors Plaza by Guild of Editors, Lai Mohammed, ya ce kada ku kwatanta lemu da tufa. Lokacin da aka sace'yan matan chibok ya kama gwamnatin PDP da laifin daukar kwanaki 18 kafin su tabbatar da sace 'yan matan. Amma a wannan lokacin mun shiga aiki cikinsa'o'i 24.

DUBA WANNAN: Shiru kake ji Hizba a Kano yayin bikin yar Hadimul Islama

Bayanan Lai Mohammed, sun tuna mani da bayanan da mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina, ya yi, ya tabbayar da rashin amincewarsu da rashin nasarar da shugaba Buhari ya samu a kan fulani makiyaya saboda lokacin jonathan ma sunyi kisan amma bai kai na yanzu ba.

Yaushe Lai Mohammed zai girmama shekarunsa ya daina karya? Shin baya jin kunya lokacin da yake fuskantar kafofin yada labarai, bayan ya yi ikirarin cewa jiragen yaki 100 ne akasa wurin neman 'yan matan Dapchi, a wata sanarwa wadda rundunar sojojin Najeriya ta karya ta. Ko da cewa Mambobin gwamnatin tasu ta san cewa Lai Mohammend makaryaci ne.

Don kaucewa shakku, ba gaskiya ba ne cewa gwamnatin Jonathan ta dauki kwanaki 18 kafin ta tabbatar da cewa an sace 'yan matan na Chibok. An sace 'yan matan Chibok a ranar 14 ga watan Afrilu, shekara ta 2014. A daidai wannan lokacin ranar 17 ga watan Afrilu, shekara ta 2014, shugaba Jonathan ya kira taron gaggawa na kasa da kasa a fadar shugaban kasa ta Aso Rock. Idan gwamnatin bata amince cewa an sace 'yan matan ba miyasa zata kira taron majalisa kare hakkin al'umma?

Yanzu fiye da mako guda kenan da aka sace 'yan matan Dapchi, shugaba Buhari ya gudanar da taron majalissar tsaro don magance halin da ake ciki? Amma bai yi ba. In takaice maka labari, don tabbatar wa 'yan Najeriya rashin adalcin shi, shugaban ya soke taron Majalisar na wannan satin.

Wane shugaba ne mai sanin ya kamat zai soke muhimmin taro irin wannan a lokacin da kasar shi ke fuskantar matsaloli haka, kaduna na fuskantar matsalar kabilanci da addini, zamfara na fuskantar kashe-kashe jama'a da 'yan fashi, benue, plateau, adamawa da taraba na fuskantar hare-haren daga Fulani makiyaya da 'yan mata 110 da aka sace a Dapchi?

Idan ka koma gwamnatin Jonathan, jojojin kasa da sojan sama sun fara neman 'yan matan tun lokacin da shugaban kasa ya kira taron na gaggawa na kasa da kasa a ranar 17 ga watan Afrilu, shekara ta 2014, tare da zartar da hanyoyin magance matsalar.

DUBA WANNAN: Hadimi yayi bayanin yadda ya boye biliyan biyar a uwar dakin Jonathan

A cewar Mr. Gaidam, sojoji a karkashin shugaba Buhari sun janye dakarun tsaro daga makarantar 'yan mata ta kimiya da fasaha, Dapchi. Wanene ya bawa sojojin umurnin su bar kula da su? Wakilin 'yan sanda yace sun mika tsaro zuwa ga 'yan sandan Najeriya. Wandannan abubuwan sune ya kamata su dami Lai Mohammed ba wai huddar gwamnatin da ta daga tuta kan yakar cin hanci da rashawa ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel