Fadar shugaban kasa tayi magana a kan satar 'yan matan Dapchi, takarar Buhari

Fadar shugaban kasa tayi magana a kan satar 'yan matan Dapchi, takarar Buhari

- Fadar shugaban kasa ta bayyana cewar shugaba Buhari zai shaidawa 'yan Najeriya matsayin takarar sa da zarar ya yanke shawara.

- Adesina ya ce ra'ayin shugaba Buhari ne ya tsaya takara ko sabanin haka

- Adesina ya ce kuskure ne a yi amfani da satar 'yan matan Dapchi wajen yin hukunci a kan kokarin gwamnatin Buhari na tabbatar da tsaro

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya ce shugaba Buhari zai sanar da 'yan Najeriya matsayin sa dangane da sake yin takarar sa a 2019 da zarar ya yanke shawara.

Adesina ya ce "da farko dai inaso jama'a su sani cewar ra'ayin shugaba Buhari ne ya sake neman shugabancin kasa ko sabanin haka. Bai yanke shawara ba ne har yanzu, kamar yadda da kan sa ya sanar. Zai sanar da jama'a da zarar ya cinma matsaya."

Fadar shugaban kasa tayi magana a kan satar 'yan matan Dapchi, takarar Buhari

Buhari da Adesina

Adesina ya ce shugaba Buhari ya shimfida aiyukan da zasu bashi kwarin gwuiwar kara yin takara. Ya lissafa nasarorin da aka samu a bangaren siyasa, tattalin arziki, tsaro da sauran su.

Adesina na wadannan kalamai ne yayin wata tattaunawa da ya yi da gidan jaridar Vanguard.

KARANTA WANNAN: Jihar Adamawa: Manyan 'yan siyasa zasu yiwa gwamna Bindo rajamu a 2019

Kakakin na shugaban kasa ya kara da cewar ba daidai bane a yi amfani da satar 'yan matan Dapchi wajen yiwa gwamnatin Buhari hukunci a kan sha'anin tsaro.

Adesina ya ce fadar shugaban kasa ta damu matuka da satar 'yan matan, sannan ya ce duk mai yin murna da satar daliban, makiyin Najeriya ne.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel