Nigerian news All categories All tags
'Yansanda sun kama lauyan bogi a jihar Imo

'Yansanda sun kama lauyan bogi a jihar Imo

- Jami'an yansandan jihar Imo sun kama lauyan bogi a jihar Imo

- Beatrice Nnamuoh ta ce tayi shekaru biyar tana aikin lauya a Najeriya

Rundunar ‘yasanda jihar Imo sun kama wata lauya bogi mai suna, Beatrice Nnamuoh, da ta dade tana aikin lauya

Legit.ng ta samu rahoton cewa, Beatrice Nnamuoh, mai shekaru,35, ta yi shekaru biyar tana aikin lauya kafin aka kama ta.

Beatrice Nnamuoh haifaffar kauyen Iyiawu ne dake jihar Anambara, amma ta na zama yankin Orlu dake jihar Imo.

'Yansanda sun kama lauyan bogi a jihar Imo

'Yansanda sun kama lauyan bogi a jihar Imo

A hirar da tayi da ‘yan jaridar PUNCH, Nnamuoh ta fada musu cewa ita ba lauyan gaskiya bace.

KU KARANTA : Babu inda kananan yara suka kada zabe a Kano – INEC ta wanke Kano

Ta ce ta karanta Sociology a jami’a kuma ta yi aiki tare da lauyoyi da yawa

Kwamishinan ‘yansandan jihar Imo,Mista Chris Ezike, a lokacin da yake zantawa da manema labaru ya fada ma su cewa, an kama mai laifin ne a yankin Orlu a bayan ta damfari wani kwastoman ta N342,000.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel