Nigerian news All categories All tags
Nakasassu za su ci moriyar tsarin gwamnatin tarayya na samar da muhalli

Nakasassu za su ci moriyar tsarin gwamnatin tarayya na samar da muhalli

- Gwamnatin tarayya ta tabbatar wa da nakasassu cewar za su ci moriyar tsarin samar da muhalli na NHP

- Sakataren ma'aikatar gidaje, lantarki, da aiyuka, Julius Olurinola, na shiyyar arewa ta tsakiya ya tabbatar da hakan

- Ya bayyana cewar duk dan Najeriya mai bukata zai iya mallakar gidan a kan farashin da gwamnatin za ta sanar a gaba

Gwamnatin tarayya ta tabbatar wa da masu nakasa cewar zasu ci moriyar tsarin samar da gidaje na NHP (National housing programme) da ake saka ran kammalawa cikin watanni shida masu zuwa.

Darektan ma'aikatar lantarki, aiyuka, da gidaje, Julius Olurinola, na shiyyar arewa ta tsakiya ya tabbatar da hakan yayin ziyarar aikin gidajen 72 da ake ginawa a Abuja.

Nakasassu za su ci moriyar tsarin gwamnatin tarayya na samar da muhalli

Nakasassu za su ci moriyar tsarin gwamnatin tarayya na samar da muhalli

Ya bayyana cewar duk dan Najeriya mai so zai iya mallakar gida a kan farashin da gwamnati za ta kayyade a nan gaba.

Olurinola ya ce aikin gina gidajen da ake yi a jihohin Najeriya 33 ya samar da aiyuka yi ga matasa.

DUBA WANNAN: Da dumin sa: An sace sakataren hukumar ilimi ta SUBEB a jihar Kano

Ya kara da cewar gwamnati ba zata tsawwala farashin gidajen ba domin dama don masu karamin karfi aka yi gidajen.

Rukunin gidajen na Abuja sun hada da gidaje masu dakin kwana daya da masu dakin kwana biyu da masu uku da kuma filin ajiyar motoci da zai iya daukan mota 50.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel