Nigerian news All categories All tags
Rikicin cikin gidan Jam’iyyar APC yayi kamari a Jihar Kogi

Rikicin cikin gidan Jam’iyyar APC yayi kamari a Jihar Kogi

- Sabon Mukaddashin Shugaban APC a Jihar Kogi ya kori Hadi Ametuo

- Kafin nan Shugabannin Jam’iyyar na Yankin Arewa sun tsige Ametuo

- Sai dai Shugaban Jam’iyyar APC na kasa bai yarda da wannan mataki ba

Mun samu labari cewa rikicin cikin gidan Jam’iyyar APC mai mulki ya kara kamari a Jihar Kogi inda ake fafatawa tsakanin bangarori biyu. Yanzu dai ta kai an kori wasu daga cikin Jam’iyyar har abada bayan dakatar da su a baya.

Rikicin cikin gidan Jam’iyyar APC yayi kamari a Jihar Kogi

Rigima ta duro Jam’iyyar APC mai mulki a Kogi

Rikicin Jam’iyyar ya dauki wani sabon fasali ne bayan bangaren da yayi wa Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello mubaya’a ya kori Shugaban Jam’iyyar na da Alhaji Hadi Ametuo da wasu manyan mukarabban sa a jiya Asabar.

KU KARANTA: Tsakanin Jam’iyyar APC da PDP wa zai yi nasara a 2019

Alhaji Ahovi Salam Ibrahim wanda shi ne ke tare da Gwamna Yahaya Bello ya bayyanawa manema labarai jiya a Garin Lokoja cewa an fatattaki Hadi Ametuo daga Jam’iyyar. Ana zargin Ametuo da yi wa APC zagon-kasa.

Kafin Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar na yanzu Ahovi Salam Ibrahim ya kori Hadi Ametuo dama Uwar-Jam’iyyar ta Arewa-maso-tsakiyar kasar ta kori mutanen Ametuo. Shugaban Jam’iyyar ta kasa dai ya musa wannan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel