Nigerian news All categories All tags
Najeriya na kokarin amshe kudinta dala biliyan ukku daga wani kamfanin mai na China

Najeriya na kokarin amshe kudinta dala biliyan ukku daga wani kamfanin mai na China

- Dala biliyan ukku dai Naira tiriliyan daya kenan

- Arzikin man Najeriya na habaka bayan da farashin man ya fara tashi

- Ga dukkan alamu kamfanin ya saba ka'idar aiki da kwangila ne

Najeriya na kokarin amshe kudinta dala biliyan ukku daga wani kamfanin mai na China

Najeriya na kokarin amshe kudinta dala biliyan ukku daga wani kamfanin mai na China

Nijeriya ta fara shirye-shiryen karban kudin ta daga hannun kamfanin Man Fetur na kasar Sin, Addax Petroleum Nigerian Limited, saboda kasa biyan kudin haraji na kimanin $3bn.

Bayan takardun shaida na kotu da majiyarmu ta gani ya nuna kudaden da ba’a biya ban a kamfanonin dake da’awa da Harkokin Kasuwancin Man Fetur da dokar gudanar da hako Man Fetur da Mota a shekara ta 2003 a kan yarjejeniyar Oil Mining Lease (OML) 123, 124, 126, da kuma 137.

A wata kara da aka shigar a gaban Alkali, Ibrahim Auta, mai lamba FHC/ABJ/CS/1099/2014, kamfanin ya nemi cigaba da amfani da yarjejeniyar daga kotu domin cigaba da yi ma Gwamnatin Nijeriya aiki.

DUBA WANNAN: Babu dan hisba ko daya da yaje kame wurin bikin gwamnoni

Tun da farkon watan Maris, an kama Babban Jami’in na kamfanin a Geneva, mai suna Zhang Yi, da kuma kwamandan Shari’a a kan zargin da akeyi ma kamfanin da aikata rashawa da cin hanci a Nijeriya. A ranar 6 ga wata Yuni, kamfanin na Addax sun yarda zasu biya Miliyan 31 na kudin Faransa wanda a kalla ya kai N11.5bn.

Kasar Faransa magance rashawa da cin hanci da aka samu wasu jami’an Nijeriya da shi. An samu wannan labarin ne ta hanyar National Resource Governance Institute (NRGI).

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel