Dokar kashe masu yada kalaman batanci: Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun yi kaca-kaca da majalissar dattawa

Dokar kashe masu yada kalaman batanci: Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun yi kaca-kaca da majalissar dattawa

- Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ki amincewa da dokar kashe masu yada kalaman batanci da majallisar dattawa ta zartar

- Dokar kashe masu yada kalaman batanci zalunci ne da rashin adalci inji kungiyar CDHR da CACOL

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam a Najeriya sun yi Allahi wadai da sabon hukuncin da majalissar Datttawa ta zartar akan masu yada kalaman batanci.

A ranar Laraba majalissar dattawa ta sanya kashe duk wanda aka kama da laifin yada kalaman batanci Najeriya.

Dokar da kakakin majalissar Dattawa, Sanata Aliyu Sabi-Abdullahi (APC Niger) ya dauki nauyin sa, ya bada shawarar kashe duk wani mai yada kalaman da za su iya janyo kashe-kashe.

Hukunci kashe masu yada kalaman batanci : Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun yi kaca-kaca da majalissar dattawa

Hukunci kashe masu yada kalaman batanci : Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun yi kaca-kaca da majalissar dattawa

Amma gamayyar kungiyoyin kare hakkin dan Adam(CDHR) da kungiyar masu rubuce-rubuce na Najeriya(CACOL) sunyi Allah wadai da wannan kudiri kuma sun kwantata shi a matsayin rashin adalci da zalunci.

KU KARANTA : Safarar mutane daga Najeriya ta karu tun da APC ta hau kan mulki - PDP

Kungiyar CDHR da CACOL sun ce kasashen duniya da dama sun daina zarta da hunkuncin kisa, bayan haka Najeriya tana da wadatacciyar hukunci da ta tanada wa masu yada kalaman batanci maimakon kisa.

Shugaban kungiyar CDHR, Malachy Ugwummadu, yace, majalissar dattawa ta na amfani da damar laifin kalaman batanci wajen ketare hakkin ‘yan Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel