Nigerian news All categories All tags
Zaben 2019: Shugabannin Majalisa sun shiryawa Shugaban kasa gadar-zare

Zaben 2019: Shugabannin Majalisa sun shiryawa Shugaban kasa gadar-zare

- Wasu Sanatoci su na kokarin ganin ba a taba tsarin zaben kasar nan ba

- Majalisar tayi barazanar takawa duk wanda ya kawo mata cikas burki

- An yi barazanar dakatar da wanda su ka sa baki daga Majalisar Dattawan

Mun samu labari cewa akwai wasu tsirarrun ‘Yan Majalisar Dattawan Najeriya da ke kokarin ganin ba a sauya tsarin zaben 2019 ba wanda wasu ke tunanin ana yunkurin yi ne domin kawowa Shugaban kasa Muhammadu Buhari cikas a zaben mai zuwa.

Zaben 2019: Shugabannin Majalisa sun shiryawa Shugaban kasa gadar-zare

Majalisar Dattawa ta sha alwashin sauya yanayin zaben 2019

Tsohon Shugaban Sanatocin Arewa watau Abdullahi Adamu ya bayyana cewa akwai akalla Sanatoci 59 da ba su yi na’am da yunkurin da ake yi na canza tsarin gudanar da zabe ba. Sai dai Majalisar ta dage da ganin cewa ta maida zaben Shugaban kasa karshe.

KU KARANTA: Wani 'Dan Majalisa ya kawo kudirin da zai sa a rika kashe jama'a

Bayan shi tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa watau Sanata Abdullahi Adamu akwai kuma Sanaata Ali Wakil (Bauchi); da Abdullahi Gumel (Jigawa); Umar Kurfi (Katsina); da Sanata Yahaya Abdullahi (Kebbi) da duk ba su yarda a taba tsarin zaben na 2019 ba.

Har wa yau akwai Sanata Garba Masi (Adamawa); da wasu Sanatocin Kudancin kasar irin Ovie Omo-Agege; Andrew Uchendu; da Benjamin Uwajimogu. Wasu ma na ganin Majalisar ba ta da wannan hurumi kuma da dama ma ba su yi na’am da hakan ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel