Nigerian news All categories All tags
Janar na Sojoji da su ka ajiye bindiga su ka shiga harkar siyasa

Janar na Sojoji da su ka ajiye bindiga su ka shiga harkar siyasa

A wannan karo mun kawo maku manyan Sojojin Najeriya da su ka tsunduma cikin harkar siyasa ne gadan-gadan bayan sun yi ritaya daga aikin bindiga. Jaridar Daily Trust ce tayi wannan nazari a karshen makon nan.

Janar na Sojoji da su ka ajiye bindiga su ka shiga harkar siyasa

Janar Babangida yayi yunkurin dawowa mulki

1. Muhammadu Buhari

Bayan Janar Muhammadu Buhari yayi mulkin sa a lokacin Soji, ya kuma dawowa siyasa a 2002 inda ya nemi takara har sau 4 kuma ya dace a 2015 ya karbi mulki a farar hula.

KU KARANTA: Wani Sanata na nema a rika rataye masu hada jama'a fada

Janar na Sojoji da su ka ajiye bindiga su ka shiga harkar siyasa

Janar Buhari da Obasanjo sun mulki Najeriya a lokacin Soji da farar hula
Source: Twitter

2. Olusegun Obasanjo

Cif Obasanjo yayi mulki a lokacin Soji shi ma kuma bayan ya fito daga kurkuku a karshen 1990s, ya karbi ragamar kasar a 1999 har zuwa 2007 kuma yana cikin masu fada-aji har gobe.

3. Ibrahim Babangida

Janar IBB yayi mulki ne bayan Janar Buhari a 1985 inda ya shafe shekaru. Ko bayan barin Babangida mulki ya shigaharkar siyasa kuma ya nemi ya zama Shugaban kasa na farar hula.

4. Abdurrahman Dambazau

Tsohon Shugaban hafsun Sojin kasan Najeriya Laftana Janar Dambazzau ya nemi yayi takarar Gwamnan Jihar Kano bayan ya ajiye kayan Soji sai dai hakan bai yiwu ba sai ya bi tafiyar Shugaba Buhari inda ya zama Ministan harkokin cikin gida.

5. TY Danjuma

Tsohon Janar din kasar nan Danjuma yana cikin masi yin yadda ya ga dama musamman a Jihar sa ta Taraba har gobe duk da tuni ya ajiye kayan yaki, Yana cikin Sojojin da su ka shiga harkar siyasa.

Bayan wadannan kuma dai akwai irin su David Mark wanda tsohon Gwamnan Soja ne kuma Shugaban Majalisar Dattawa da wasu Sanatocin irin su Jerimiah Useini, Jonah Jang, Murtala Nyako, da su Ike Nwachukwu da sauran su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel