Nigerian news All categories All tags
Shugaba Buhari ya nemi kasar Birtaniya ta binciki gidajen Ekweremadu da Saraki dake birnin Landan

Shugaba Buhari ya nemi kasar Birtaniya ta binciki gidajen Ekweremadu da Saraki dake birnin Landan

Rahotanni da sanadin Sahara Reporters sun bayyana cewa, hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta kasar Birtaniya, za ta shiga cikin bincike kan yadda Bukola Saraki da Ike Ekweremadu suka mallaki gidaje da kadarori na alfarma a birnin Landan.

Wannan bincike zai wakana ne sakamakon umarni da kuma bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari, dangane da yadda shugaban majalisar dattawa da mataimakin sa suka mallaki wasu manyan gidaje na alfarma a kasar ta Birtaniya.

Saraki dai ya mallaki wasu gidaje biyu na alfarma da kudin su ya kai kimanin Fan Miliyan 15 a yayin da yake gwamnan jihar Kwara kuma hadimi na musamman ga tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.

Ekweremadu da Saraki

Ekweremadu da Saraki

Mataimakin shugaban majalisar Ekweremadu, ya mallaki wasu kadarori na kimanin Fan miliyan 4 a yayin da yake kujerar sakatare kuma shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Enugu.

KARANTA KUMA: Da sai mun iya hana harin Dapchi - Peace Corps ga Buhari

Legit.ng da sanadin Sahara Reporters ta bayyana cewa, shugabanni biyu na majalisar sun yi amfani da wasu hanyoyi na basaja wajen mallakar wannan kadarori a kasar ta Birtaniya.

Jaridar ta kuma ruwaito cewa, Farfesa Ben Nwabueze, ya soki yadda masu karancin ilimi da rikicin tsufa ke rike da madafun iko a kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel