Nigerian news All categories All tags
Atiku zai bayyana matsayar takarar sa a sati biyu masu zuwa

Atiku zai bayyana matsayar takarar sa a sati biyu masu zuwa

- Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce sai sanar da al'umma shawarar da ya yanke game da batun tsayawa takarar 2019 cikin sati biyu

- Atiku ya bayyana hakan ne ranar Asabar a wajen kaddamar da wata shirri na tallata manufofin sa a garin Abuja

- Atiku ya shawarci yan Najeriya cewa lokaci ya yi da ya dace su kori wanda suka kasa cika musu alkawuran da suka dauka musu

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma Wazirin Adamawa Atiku Abubakar ya ce zai bayyana wa duniya matsayar sa game da tsayawa takarar zaben shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP nan da makonni biyu masu zuwa.

Atiku zai bayyana ko zai tsaya ko ya fasa tsayawa takara a 2019 a PDP

Atiku zai bayyana ko zai tsaya ko ya fasa tsayawa takara a 2019 a PDP

Ya bayyana hakan ne a ranar Asabar wajen kaddamar da wata shiri na musamman don tallata manufofin sa da akayi wa lakabi da 'Street to Street (SSSI) da kuma zaben shuwagabanin shirin na jihohi da yankunan karkashin Shugaban shirin na kasa Wabara Emeka Gerald.

KU KARANTA: An bude sashen koyar da kasuwanci a Jami'ar Bayero da Dangote ya gina

Atiku ya samu wakilcin Direktan gidauniyar Atiku cares kuma Shugaban Kungiyar matasa masu goyon bayan Atiku, Aliyu Bin Abbas.

A cewar Aliyu, tsohon mataimakin shugaban kasar ya kusa zubar da hawaye saboda irin kauna da goyon baya da al'umma ke nuna masa a duk fadin kasar nan musamman game da niyyar sa na tsayawa takarar zabe a 2015.

"Lokaci ya yi da yan Najeriya za su yi kori wandanda suka kasa tabuka musu komai sai dai farfaganda da nuna halin ko in kula ga jama'a," inji shi.

A jawabin sa, Jagoran masanna na kamfe din Atiku, Theophilus Ohoba ya bayyana cewa canjin da gwamnatin baya tayi wa yan Najeriya alkawari bashi da amfani idan akayi la'akari da matsanan cin halin rayuwa da talakawa suke ciki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel