Nigerian news All categories All tags
An kama mutum 18 da ke da hannu cikin rikicin addinin a Jihar Kaduna

An kama mutum 18 da ke da hannu cikin rikicin addinin a Jihar Kaduna

- Hukumomin tsaro sunyi nasarar cafke wasu mutane da ake zargin da hannu cikin rikicin Kasuwar Magani ta Jihar Kaduna

- Wannan sanarwan ta fito ne daga bakin rundunar tsaro ta hadin gwiwa a yayin wata ziyara da suka kai garin na Kasuwar Magani

- Jami'an tsaron sunyi kira ga al'ummar jihar su rungumi zaman lafiya kuma su cigaba da bin doka da oda

Jami'an tsaro sunyi nasarar kama mutane 18 da ake zargi da hannu a ruruta wutar rikicin addini da ya faru a garin Kasuwar Magani da ke karamar hukumar Kajuru na Jihar Kaduna. Rikicin ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kone-konen gidaje da wasu dukiyoyin al'umma.

An kama mutum 18 da ke da hannu cikin rikicin addinin a Jihar Kaduna

An kama mutum 18 da ke da hannu cikin rikicin addinin a Jihar Kaduna

Sanarwan hakan ta fito ne daga bakin rundunar hadin gwiwa ta tsaro wanda ta kunshi Shugaban Dakarun Soji na jihar Kaduna, Kwamishinan yan sanda da kuma shugaban Jami'an tsaro na farin DSS yayin da suka kai wata ziyara garin na Kasuwan Magani.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun sako iyalan ma'aikacin VOA bayan ya biya N2m

Shuwagabanin hukumomin tsaron sun ziyarci garin ne don su gane wa idanun su irin ta'addin da aka tafka kana su tattauna da jama'ar garin kuma su karbi bayanai daga bangarorin hukumomin tsaro da ke garin.

Hadimin gwamnan jihar Kaduna, Mista Samuel Aruwan ya bayyana cewa gwamnatin jihar karkashin jagorancin Malam Nasiru El-Rufai da dau alwashin zakulo da hukunta wanda sukayi sanadiyar tashin fitinar don hakan ya zama darasi ga sauran al'umma.

Gwamnatin kuma ba za tayi kasa a gwiwa ba wajen cigaba da samar da tsaro da rayyuka da dukiyoyin al'ummar kana yana mai kira da mutane su kasance masu kaunar zaman lafiya da biyaya ga doka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel