Nigerian news All categories All tags
Sabuwar gwamnati a Africa ta Kudu zata kwace gonakin turawa ta mikawa talakawa bakaken fata

Sabuwar gwamnati a Africa ta Kudu zata kwace gonakin turawa ta mikawa talakawa bakaken fata

- Sabuwar gwamnati a Kudanccin Afirka zata yi koyi da Zimbabwe

- Afirka ta sha mulkin mallaka a hannnun Turawa

- Har yanzu wasu kasashen kudanci na cikin matsi saboda kwace arziki da Turawa masu kaka-gida suka yi

Sabuwar gwamnati a Africa ta Kudu zata kwace gonakin turawa ta mikawa talakawa bakaken fata

Sabuwar gwamnati a Africa ta Kudu zata kwace gonakin turawa ta mikawa talakawa bakaken fata

Robert Mugabe, shugaban kasar Afirka ta kudu, daga jam'iyya mai mulki ANC, Cyril Ramaphoma, dan kishin kasa kuma tsohon mai fada da turawa masu kaka-gida da mulkin danne bakake, ya bayyana cewa dole ne gwamnati ta kwace manyan filaye, dazuka da gonaki daga farare turawa ta rabawa baqaqen fata.

A kokarin da gwamnatocin yankin kudancin Afirka keyi, na dawo da arziki hannun 'yan asalin Afirka, ba jikokin turawa da aka bari da dumbin dukiyar Afirka bayan mulkin mallaka ba, musamman kasashen kudanci nahiyar, kasar Zimbabwe karkashin Mugabe, tasha bakar wahala.

Ta sha takunkummi saboda kwatar manyan gonaki da baiwa talakawa bakake, inda tace gonakin na kakanninsu ne ba na turawa ba. Takunkumai da suka ruguza tattalin arzikin kasar.

DUBA WANNAN: An kashe ma'aikatan UN a jihar Borno

A yanzu dai sai gashi kasarr Afirka ta Kudu itama ta dauki aniyar hakan. Su dai Turawan su ke da manyan gonaki da kakanninsu suka kwace wa baqaqe suka kuma karkashe su.

Dawo da gonakin zai iya kawo wa bakaken arziki da tattalin arziki, sai dai kasar na iya fuskantar fushin Turawan yamma. Su kuma baqaqen basu yi ilimin boko ba, wanda hakan ka iya durkusar da arzikin kasar da samuwar abinci.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel