'Yan sanda sun dakile yunkurin wata hari da 'yan bindiga suka kai Jihar Zamfara

'Yan sanda sun dakile yunkurin wata hari da 'yan bindiga suka kai Jihar Zamfara

- Rundunar Yan sandan reshen jihar Zamfara tayi nasarar dakile wata yunkurin hari da yan bindiga suka kawo a garin Wuya

- 'Yan bindigan sun shigo garin ne a kan babura dauke da bindigogi amma sukayi kacibus da jami'an yan sanda inda suka gabza musayar wuta

- Yan sandan sun ci galaba a kan su har ma sunyi nasarar kama daya daga cikin yan bindigan

Rundunar yan sandan ta Jihar Zamfara ta ce jami'an ta sun dakile wata hari da wasu yan dadi bindiga suka kai garin Wuya da ke karamar hukumar Anka da ke jihar kuma sunyi nasarar cafke daya daga cikin su.

'Yan sanda sun dakile yunkurin wata hari da 'yan bindiga suka kai Jihar Zamfara

'Yan sanda sun dakile yunkurin wata hari da 'yan bindiga suka kai Jihar Zamfara

Sanarwan ta fito ne ta bakin kakakin rundunar yan sandan, DSP Muhammad Shehu wanda ya yin da ya ke ganawa da manema labarai ranar Asabar a garin Gusau kamar yadda NAN ta ruwaito.

KU KARANTA: An kama mutum 18 da ke da hannu cikin rikicin addinin a Jihar Kaduna

A cewar Shehu, Yan bindigan sun shigo garin na Wuya ne da babura da yawa don suyi fashi amma suka ci karo da jami'an rundunar wanda suka bude musu wuta, inda suka raunana wasu sannan saura suka gudu cikin daji.

"An kama daya daga cikin yan bindigan tare da bindiga kirar AK 47 da alburusai," inji shi

Shehu ya yi kira ga al'umma su cigaba da bawa rundunar yan sandan da sauran hukumomin tsaro hadin kai ta hanyar basu bayyanai masu amfani game da bata garin da kuma inda suke buya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel