Masu garkuwa da mutane sun sako iyalan ma'aikacin VOA bayan ya biya N2m

Masu garkuwa da mutane sun sako iyalan ma'aikacin VOA bayan ya biya N2m

- Ma'aikacin VOA da aka sace iyalansa, Malam Nasir Birnin Yero ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun sako su

- An sako iyalan na sa ne a daren Juma'a bayan ya biya su kudin fansa naira miliyan two

- Birnin Yero ya bayyana cewa iyalan nasa suna cikin koshin lafiya lokacin da aka sako su

Masu garkuwa da mutane da suka sace iyalan ma'aikacin kamfanin yadda labarai na Voice of America (VOA), Malam Nasir Birnin Yero sun sako su bayan an biya su kudin fansa naira miliyan biyu kamar yadda kamfanin dillanci labarai NAN ta ruwaito.

Sun dai sace iyalan Malam Nasir ne a ranar Laraba, 28 ga watan Fabrairu inda suka halaka wani ma'aikacin hukumar kare haddura na kasa FRSC wanda ya yi yunkurin taimakawa iyalan kafin a sace su.

Masu garkuwa da mutane sun saka iyalan ma'aikacin jaridar VOA bayan ya biya N2m

Masu garkuwa da mutane sun saka iyalan ma'aikacin jaridar VOA bayan ya biya N2m

KU KARANTA: 2019: Wasu tsaffin ministoci da jiga-jigan jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa SDP

Legit.ng ta gano cewa Yero ya bayyana cewa an sako iyalan nasa ne a ranar daren Juma'a 2 ga watan Maris a garin Sabon Birnin da ke kusa da filin tashin jiragen sama na Kaduna.

"Masu garkuwa da mutanen sun tuntube ni kuma sun bukaci a biya su naira miliyan 12 kafin su sako iyalan nawa.

"Sun fada min cewa ni suka yi niyyar sacewa amma basu same ni ba, kuma idan ina son ganin iyalai ne, sai na biya kudin fansar.

"Amma daga baya mun roki su kuma suka amince mu biya naira miliyan 2 wanda yan uwa da abokan arziki suka taimaka wajen hada kudin kuma muka biya." inji shi.

Ya kuma ce iyalan nasa na cikin koshin lafiya lokacin da aka sako su.

A baya, Legit.ng kawo muku rahoton yadda masu garkuwa da mutane suka sace iyalan ma'aikacin kamfanin yadda labarai na VOA a gidan sa misalin karfe 1.30 na dare.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel