Nigerian news All categories All tags
IBB da Danjuma sun shiga ganawar sirrance a birnin Minna

IBB da Danjuma sun shiga ganawar sirrance a birnin Minna

Tsohon shugaban kasa na mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya yi wata ganawar sirri da wani tsohon soja kuma gawurtaccen Attajiri, Janar Theophilus Danjuma, a babban gidan sa dake birnin Minna na jihar Neja.

Da sanadin rahotanni na ranar Juma'ar da ta gabata, Jaridar The Punch ta ruwaito cewa wannan ganawar ta dauki tsawon awanni uku, bayan Danjuma ya sauka a filin jirga sama na Minna da misalin karfe 11.45 na safe kuma ya dirfafi gidan tsohon shugaban kasa Babangida.

Janar Ibrahim Badamasi Babangida

Janar Ibrahim Badamasi Babangida

Legit.ng ta fahimci cewa, Danjuma wanda ya yiwa manema labari Dan-waken zagaye ya kama hanyar sa ta zuwa filin jirgin saman da misalin karfe 4.05 na yammacin ranar.

KARANTA KUMA: An dakatar da ma'aikatan lafiya 4 da laifin bude kwakwalwar wani mara lafiya bisa kuskure

Wata majiyar rahoto ta bayyana cewa, tsaffin sojin sun tattauna ne kan batutuwa da suka shafi tsaro da kuma siyasar kasar nan.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wani dattijo ya yi Odar shinkafar bera tun daga kasar Sin domin kashe iyayen sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel