Nigerian news All categories All tags
APC ta ware N15bn don gudanar ta tarurruka da zaben Osun da Ekiti

APC ta ware N15bn don gudanar ta tarurruka da zaben Osun da Ekiti

- Jam'iyyar APC ta gabatar da kasafin kudin ta na shekarar 2018

- Jam'iyyar ta gabatar da kasafin kudin ne a taron kwamitin zartarwa na jam'iyyar da aka gudanar a fadar Aso Villa

- Jam'iyyar ta bayar da kididigan yadda za'a samo kudaden da za'a gudanar da ayyukan kafin karshen 2018

Gabanin zabukkan gwamnoni a jihohin Ekiti da Osun da kuma babban zaben kasa na 2019, jam'iyyar APC ta gabatar da kasafin kudi naira biliyan 14.82 don gudanar da harkokin jam'iyyar.

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa wata majiya daga jam'iyyar ta APC ta bayyana cewa kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ta gabatar da kasafin kudin ne a ranar Litinin a taron kwamitin zartarwa na Jam'iyyar da aka gudanar a fadar Aso Villa da ke Abuja.

APC ta ware N15bn don gudanar ta tarurruka da zaben Osun da Ekiti

APC ta ware N15bn don gudanar ta tarurruka da zaben Osun da Ekiti

KU KARANTA: 2019: Wasu tsaffin ministoci da jiga-jigan jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa SDP

Kunshe cikin takardar da aka gabatar mai taken 'Rahoton kudade na shekarun 2016, 2017 da kasafin kudi na 2018' wanda ke dauke sa hannun ma'ajin jam'iyyar na kasa, Alh. Bala Muhammed Gwagwarwa, jam'iyyar ta ce tana sa ran samun N5.86bn daga siyar da form din takara, N3.4bn daga gudunmawa, N4.2bn daga kudaden rajistan mambobi, N1bn daga siyar da kati sannan N0.304bn daga masu rike da mukamai a jam'iyyar.

Jam'iyyar har ila yau, ta bayyana cewa za'a bukaci zunzurutun kudi N1.3bn don shirya gangamin taron shekara na jam'iyyar da kuma wani karin N1 bn don wayar da kan al'umma a kafafen yadda labarai.

Hakazallika, jam'iyyar karkashin jagorancin Cif John Odigie-Oyegun za tayi amfani da asusu daya da kuma fasahar biyan kudi na Remita ta yanan gizo don karbar kudin mambobi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel