Nigerian news All categories All tags
Sabon rikici a APC: An bukaci kotu ta soke karin wa'adin da aka yi wa Oyegun da mukarraban sa

Sabon rikici a APC: An bukaci kotu ta soke karin wa'adin da aka yi wa Oyegun da mukarraban sa

Wani jigo a jam'iyyar All Progressives Congress, APC mai mulki a jihar Imo dake a kudu maso gabashin kasar nan, mai suna Mista Okere Uzochukwu ya shigar da jam'iyyar sa kara kara a wata kotun gwamnatin tarayya dake zaman ta a garin Abuja.

Mista Okere, kamar yadda muka samua cikin karar ya bukaci kotun da ta soke karin wa'adin mulkin da aka yi wa shugaban jam'iyyar APC da mukarraban sa.

Sabon rikici a APC: An bukaci kotu ta soke karin wa'adin da aka yi wa Oyegun da mukarraban sa

Sabon rikici a APC: An bukaci kotu ta soke karin wa'adin da aka yi wa Oyegun da mukarraban sa

KU KARANTA: Hotunan jaririya mai hannu 4 da kafa 3 da aka haifa a Kaduna

Mun samu cewa dai wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wani taron jiga-jigan jam'iyyar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta inda kuma daga karshe aka amince da karawa dukkan shugabannin jam'iyyar a fadin kasar wa'adin watanni 12.

A wani labarin kuma, Shugaban hadakar manyan kungiyoyin matasa akalla 70 karkashin inuwar babbar kungiya mai suna Kwara Rescue Alliance mai suna Abdulsalam Ibrahim a jiya juma'a ya bayyana cewa sun daura damarar ganin lallai shugaban majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki ya dawo gida a zabe mai zuwa na 2019.

Abdulsalam dai ya bayyana rashin sahihi, kuma kyakkyawan wakilci a matsayin wani babban dalilin da ya sa suke so lallai sai Sanatan ya dawo gida a zaben mai zuwa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel