Hare-hare: Shugaba Buhari ya kara zaburar da jami'an tsaron Najeriya

Hare-hare: Shugaba Buhari ya kara zaburar da jami'an tsaron Najeriya

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kwarmata wa 'yan Najeriya kadan daga cikin batutuwan da suka tattauna da jami'an tsaron kasar nan yayin tattaunawar sirrin da suka yi a fadar shugaban kasar dake a unguwar Villa, babban birnin tarayyar Najeriya.

Shugaban kasar ya sanarwa da 'yan Najeriya cewar ya umurci dukkan jami'an tsaron da su kara zage dantse wajen ganin sun kara azama wajen bankado laifuka da masu yunkurin aikata su tun kafin ma su kai ga aikata su.

Hare-hare: Shugaba Buhari ya kara zaburar da jami'an tsaron Najeriya

Hare-hare: Shugaba Buhari ya kara zaburar da jami'an tsaron Najeriya

KU KARANTA: Kotun koli ta kori karar da Dasuki ya shigar

Legit.ng ta samu cewa shugaban yayi wannan bayanin ne a cikin wani dogayen jerin sakwanni da yayi ta shafin sa na dandalin sada zumunta na Tuwita.

A wani labarin kuma, Kotun koli ta kasa ta kawo karshen takaddamar shari'ar da ake yi ta cigaba da tsare tsohon mai ba shugaban kasa shawara ta fannin tsaro, Kanal Sambo Dasuki da ake cigaba da yi a wani boyayyen wuri na musamman.

A cikin wani hukunci da kotun ta yanke a ta bakin babban alkalin kotun Mai shari'a Ajembi Eko a jiya ya bayyana cewa kotun ta gano cewa ba hukumar EFCC ce ba ke dauke da alhakin cigaba da tsare Kanal Dasuki din.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel