Nigerian news All categories All tags
Tsare Dasuki: Kotun Allah-ya-isa ta ce hukumar EFCC ba ta da laifi

Tsare Dasuki: Kotun Allah-ya-isa ta ce hukumar EFCC ba ta da laifi

Kotun koli ta kasa ta kawo karshen takaddamar shari'ar da ake yi ta cigaba da tsare tsohon mai ba shugaban kasa shawara ta fannin tsaro, Kanal Sambo Dasuki da ake cigaba da yi a wani boyayyen wuri na musamman.

A cikin wani hukunci da kotun ta yanke a ta bakin babban alkalin kotun Mai shari'a Ajembi Eko a jiya ya bayyana cewa kotun ta gano cewa ba hukumar EFCC ce ba ke dauke da alhakin cigaba da tsare Kanal Dasuki din.

Tsare Dasuki: Kotun Allah-ya-isa ta ce hukumar EFCC ba ta da laifi

Tsare Dasuki: Kotun Allah-ya-isa ta ce hukumar EFCC ba ta da laifi

KU KARANTA: An ci zarafin dan jarida a jihar Akwa Ibom

Legit.ng ta samu cewa kotun ta bayyana a binciken da ta yi cewar hukumar 'yan sandan farin kaya ta DSS ce ke cigaba da tsare shi bisa zargin da ake yi masa na badakalar kudaden makamai da suka kai Dalar amurka biliyan biyu.

A wani labarin kuma, Majalisar zartaswar Najeriya dake da hada da shugaban kasa Muhammadu Buhari, mataimakin sa da ministoci da ma wasu manyan ma'aikatan kasar sun amince da ware makudan kudade domin kashewa wajen bayar da tsaro a gabar tekunan Najeriya.

Ministan sufuri na kasar kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Mista Rotimi Amaechi shine ya sanar da hakan, inda ya bayyana cewa gwamnatin ta ware kimanin Naira biliyan 59.86 domin gudanar da aikin.

Idan ka na da wasu shawarwari ko bukatar bamu labari, to tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel