Nigerian news All categories All tags
Tsaro: Majalisar zartaswa ta amince da Naira 59.86 biliyan don tsare gabar ruwan Najeriya

Tsaro: Majalisar zartaswa ta amince da Naira 59.86 biliyan don tsare gabar ruwan Najeriya

Majalisar zartaswar Najeriya dake da hada da shugaban kasa Muhammadu Buhari, mataimakin sa da ministoci da ma wasu manyan ma'aikatan kasar sun amince da ware makudan kudade domin kashewa wajen bayar da tsaro a gabar tekunan Najeriya.

Ministan sufuri na kasar kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Mista Rotimi Amaechi shine ya sanar da hakan, inda ya bayyana cewa gwamnatin ta ware kimanin Naira biliyan 59.86 domin gudanar da aikin.

Tsaro: Majalisar zartaswa ta amince da Naira 59.86 biliyan don tsare gabar ruwan Najeriya

Tsaro: Majalisar zartaswa ta amince da Naira 59.86 biliyan don tsare gabar ruwan Najeriya

KU KARANTA: Ana sa ran Buhari yaje Kano, yau

Ministan dai yayi wannan bayanin ne a cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta sufuri ta fitar dauke da sa hannun sa yayin da ake gudanar da wani muhimmin taro na masu ruwa da tsaki a garin Warri, jihar Delta.

A wani labarin kuma, Kotun koli ta kasa ta kawo karshen takaddamar shari'ar da ake yi ta cigaba da tsare tsohon mai ba shugaban kasa shawara ta fannin tsaro, Kanal Sambo Dasuki da ake cigaba da yi a wani boyayyen wuri na musamman.

A cikin wani hukunci da kotun ta yanke a ta bakin babban alkalin kotun Mai shari'a Ajembi Eko a jiya ya bayyana cewa kotun ta gano cewa ba hukumar EFCC ce ba ke dauke da alhakin cigaba da tsare Kanal Dasuki din.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel