Nigerian news All categories All tags
Wani Dattijo ya yi Odar gubar Bera tun daga kasar Sin domin Kashe Iyayen sa

Wani Dattijo ya yi Odar gubar Bera tun daga kasar Sin domin Kashe Iyayen sa

A ranar Juma'ar da ta gabata ne wata Kotun Birnin Ingolstadt ta kasar Jamus, ta zartar da hukuncin dauri na shekaru 9 da rabi kan wani manomi da laifin yunkuri na kashe iyayen sa da shinkafar bera.

Wannan Kotu dai ta la'anci wannan mutum mai shekaru 53 a duniya, inda ta kama shi da laifi dumu-dumu na yunkurin kisa.

A cewar Alkalan Kotun, wannan dattijo dai ya yi Odar shinkafar bera tun daga kasar Sin, kuma ya gauraya ta cikin abincin gyatuman sa tun a karshen shekarar 2016 da ta gabata.

Wani Dattijo ya yi Odar gubar Bera tun daga kasar Sin domin Kashe Iyayen sa

Wani Dattijo ya yi Odar gubar Bera tun daga kasar Sin domin Kashe Iyayen sa

Tarayyar jaridun Leadership da kuma The Punch sun ruwaito cewa, Likitoci na asibitin Jami'ar Regensburg sun nuna kwarewar aikin su, inda suka ceto rayuwar Mahaifin sa mai kimanin shekaru 81 da kuma Mahaifiyarsa mai shekaru 77 a duniya.

KARANTA KUMA: Gowon cike da mamaki: Obasanjo ya bayyana wani Sirri kan tsohuwar gwamnatin su shekaru 43 baya

Sai dai wannan mutum ya shaidawa Kotun cewa, ko kadan bai nufaci kashe iyayen sa ba domin kuwa ya watsar da wannan shinkafa ta bera bayan ta karaso gareshi, inda ya zargi wata 'yar uwa ta sa da aikata wannan mugun nufi.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya fayyace sirrin wani Tuggu da suka kulla shekaru 43 da suka gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel