Nigerian news All categories All tags
Sheikh Ba: Ya jinjina wa shugaba Erdogan da irin taimakon da yake bawa al'ummar musulmi

Sheikh Ba: Ya jinjina wa shugaba Erdogan da irin taimakon da yake bawa al'ummar musulmi

- Sheikh Ba na kasar Senegal ya jinjinawa shugaban kasar Turkiyya bisa taimakon da yake yiwa al'ummar musulmi

- Ya ce shugaba Erdogan shine mutum na farko da yake kokarin kawo musulmi dauki a duk lokacin da yaji cewar sun shiga matsala

- Ya ce kasar Somaliya da kasar Myamar sune kasashe abin misali akan irin taimakon da yayi musu

Sheikh Ba: ya jinjina wa shugaba Erdogan da irin taimakon da yake bawa al'ummar musulmi

Sheikh Ba: ya jinjina wa shugaba Erdogan da irin taimakon da yake bawa al'ummar musulmi

Wani shahararren malamin addinin Islama na kasar Senegal, Abdullahi Usman Ba, ya rubuta wata takarda don jinjina wa shugaba Erdogan na kasar Turkey game da namijin kokarin da yake yiwa duniyar musulunci.

DUBA WANNAN: 'Yan Boko Haram sun kashe ma'aikatan majalisar dinkin duniya a Borno

Malamin wanda ya gaisa da shugaban kasar Turkiyya din, a yayin wata ziyara da shugaban ya kai kasar Senegal.

Malamin ya ce: “Shugabanmu Erdogan muna kaunarka saboda Allah. Domin duk lokacin da wani tashin hankali ya afku a yankin musulmai, kai kake zama mutum na farko da ke garzayowa don kawo wa mutanen mu dauki. Somaliya da Myanmar sune manyan misalan da zan bayar,” in ji shi.

Sannan yayi mashi addu’ar Allah ya kara karfafa mashi gwiwa akan kokarin da yake yiwa al’ummar musulmi da kuma duniya baki daya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel