Nigerian news All categories All tags
'Yan Boko Haram sun kashe ma'aikatan majalisar dinkin duniya a Borno

'Yan Boko Haram sun kashe ma'aikatan majalisar dinkin duniya a Borno

- An kashe ma'aikatan majalisar dinkin duniya a Najeriya

- 'Yan kungiyar boko haram sun kai hari sansanin sojoji dake garin Rann a jihar Borno

- Sun kashe ma'aikatan majalisar dinkin duniya guda uku kamar yanda kungiyar MDD ta bayyana

'Yan Boko Haram sun kashe ma'aikatan majalisar dinkin duniya a Borno

'Yan Boko Haram sun kashe ma'aikatan majalisar dinkin duniya a Borno

Wasu ma’aikatan majalisar dinkin duniya su uku sun rasa rayukan su a lokacin da ‘yan ta’addan boko haram suka kai wani mummunan hari sansanin sojoji dake garin Rann a jihar Borno.

Mai Magana da yawun kungiyar MDD ta tabbatar da afkuwar hakan ga manema labarai.

DUBA WANNAN: Majalisar wakilai tana tuhumar kamfanoni 31 bisa zargin su da cin hanci da rashawa

Ta kara da cewa akwai yiwuwar wani jami’in shima ya rasa ransa, sannan ta bayyana cewa an sace daya daga cikin ma’aikatan MDD din.

Ta tabbatar wa da manema labarai cewar dukkan wadanda aka kashe din ‘yan Najeriya ne da suke aiki da MDD.

Wata majiya ta bayyana wa manema cewar maharan ‘yan kungiyar boko haram ne, wadanda suke kai hare-hare a yankin.

A makon daya gabata mayakan boko haram din suka kai hari wata makarantar sakandare dake garin Dapchi, a jihar Yobe, inda suka yi gaba da dalibai mata fiye da 100, har zuwa yanzu dai ba a san halin da suke ciki ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel