Sanatoci na kiyayya da ni ne saboda ina aikina yadda ya kamata – Inji Jagoran yaƙi da ɓarayin gwamnati

Sanatoci na kiyayya da ni ne saboda ina aikina yadda ya kamata – Inji Jagoran yaƙi da ɓarayin gwamnati

Shugaban hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, Ibrahim Magu, ya danganta rashin amincewarsa da yan majalisar dattawa su ka yi ga irin aikin da yake yi.

Jaridar The Cable ta ruwaito har sau biyu majalisar dattawa na yin watsi da Magu da nufin tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar, ba na rikon kwaryar da yake a yanzu ba, inda suka kafa hujjar watsi da shi ga rahoton da suka samu daga hukumar DSS.

KU KARANTA: Alakar Diflomasiyya: Sakataren gwamnatin kasar Amurka zai kawo ziyara Najeriya

Dayake tattunawa da gidan Talabijin na Channels, Magu yace majalisar dattawa suna yi masa bita da kulli ne saboda yana aiki tukuru, wanda yace hakan bai shafi aikinsa ba, face ma kwarin giwa da hakan ya kara masa, kuma ba zai ja da baya ba.

Sanatoci na kiyayya da ni ne saboda ina aikina yadda ya kamata – Inji Jagoran yaƙi da ɓarayin gwamnati

Magui

“Bana tunanin wannan matsalar zai kawo mana tsaiko a aikin da muke yi, illa ma kwarin gwiwa da haka ya bani, rashin amincewar da suka yi min ya nuna ina aiki yadda ya kamata. A irin wannan aikin da muke yi, idan kaga majalisa sun tantanceka da hanzari, toh akwai matsala kenan.” Inji shi.

Da aka tambaye shi mai yasa akansa ne aka fara samun matsalar, sai yace hakan ya faru ne saboda watakila suna jin dadin sauran ne, saboda a yanzu haka da dama daga cikin wadanda muke bincika suna majalisun dokokin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel