Nigerian news All categories All tags
Ya kamata Najeriya ta fara kaddamar da hukuncin kisa akan dillaln miyagun kwayoyi – Inji Bala Lau

Ya kamata Najeriya ta fara kaddamar da hukuncin kisa akan dillaln miyagun kwayoyi – Inji Bala Lau

Shugaban kungiyar Izala, Sheikh Abdullahi BalaLau ya shawarci gwamnatn tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta yi koyi da kasar Saudiyya wajen zartar da hukuncin kisa akan duk wanda aka kama da safarar kwayoyi da dillalanta.

Legit.ng ta ruwaito Bala Lau ya bayyana haka ne duba da irin matsalolin da kwayoyi ke haifar ma matasan Najeriya, musamman na yankin Arewa, ta hanyar bata musu kwakwalwa da tunani.

KU KARANTA: Alakar Diflomasiyya: Sakataren gwamnatin kasar Amurka zai kawo ziyara Najeriya

Bala Lau yace ya zama wajibi ya yi wannan kira ga gwamnati, duba da muguwar rawar da dillalan miyagun kwayoyi ke takawa wajen jefa rayuwar matasan Najeriya cikin hadarin gaske, wanda yake sanadiyyar lalata su, ba zasu amfani kasar ba.

Sheikh Lau ya cigaba da fadin cewa saboda haka ne ya sanya gwamnatin kasar Saudiyya ta ke zartar da hukuncin kisa kan duk wanda ta kama da aikin dillancin miyagun kwayoyi, saboda a cewarsu, duk mai wannan sana’ar na da nufin kashe cigaba da kasar nan, duba da matasa su ne kashin bayan cigaban kowane kasa.

Daga karshe yace wannan tsatstsauran mataki da kasar Saudiyya ta dauka ya taimaka mata matuka waken samar da al’umma ta gari, don haka idan Najeriya ta bi sawun kasar Saudiyya, za’a samu biyan bukata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel