Nigerian news All categories All tags
Zamu hukunta duk wadanda suka yi sakaci har aka sace yan matan Dapchi – Inji Buhari

Zamu hukunta duk wadanda suka yi sakaci har aka sace yan matan Dapchi – Inji Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dau alwashin hukunta duk jami’I ko wata hukumar da aka kamata da sakaci a bakin aikinta, wand ya yi sanadiyyar daliban kwalejin yan matan kwalejin kimiyya da fasaha na garin Dapchi.

An sace daliban ne dai a ranar 19 ga watan Feburairu a makarantarsu dake karamar hukumar Busari na jihar Yobe, har su 110, inda ake zargin kungiyar yan ta’addan Boko Haram, tsagin yaron Muhammadu Yusuf, Abu Musab Albarnawi da tafka ta’asan.

KU KARANTA: Wani abu guda ɗaya rak da Ganduje ke bukata daga Kwankwaso matukar yana son ayi Sulhu

Mashawarcib shugaba Buhari a kan harkar tsaro, Babagana Munguno ne ya bayyana haka a ranar Juma’a 2 ga watan Maris a yayin rantsar da kwamitin mutane 12 da aka daura musu hakkin binciko musabbabin sace yan matan, da kuma yadda hakan ta faru.

Zamu hukunta duk wadanda suka yi sakaci har aka sace yan matan Dapchi – Inji Buhari

Yan matan Dapchi

“Zamu yi amfani da kudin yan Najeriya ne wajen gudanar da wannan muhimmin aiki, don haka ya zama wajibi a su san sakamakon aikin da muka yi, kuma ba zamu lamunci a sakaya sunayen masu hannu cikinw wannan lamarin ba, ko kuma a daga musu kafa. Ya zama dole a fallasa duk masu hannu a ciki.” Inji Munguno.

Legit.ng ta ruwaito Munguno ya nuna bacin ransa da cecekucen da aka dinga yi tsakanin rundunar Sojin Najeriya da rundunar Yansandan Najeriya game da sakacin wanene ya janyo sace yan matan, inda yace hakan abin kunya ne ga shugaban kasa.

Daga karshe Munguno ya tabbatar ma kwamitin cewa rahoton su zai taimaka wajen gano yadda satar yan matan Chibok ya kasance. Kwamitin dai ya kunshi wakilan hukumar leken asiri, NIA, hukumar binciken tsaro na fasaha, DIA, rundunar Yansanda, hukumar tsaro ta sirri, DSS, da rundunar Sojojin sama, kasa da na ruwa, sai kuma NSCDC da wakili daga ofishin Munguno.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel