Hukumar INEC ta gano sunayen bakin haure a masu rijistan zabe

Hukumar INEC ta gano sunayen bakin haure a masu rijistan zabe

A ranar Juma’a, 2 ga watan Maris, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewa ta gano sunayen yan kasar waje 299 a cikin wadanda sukayi rijistan zabe.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana hakan a wani taron tuntuba na hukumar tare da hukumomin tsaro a Abuja.

Yakubu ya bayyana cewa an gano sunayen ne ta hanyar bayanai da hukumar dake kula da masu shige da fice a kasar ta bayar.

Ya bayyana cewa yin rijistan zabe da kada kuri’u hakki ne na al’umman kasar Najeriya inda doka ta cire baki.

Hukumar INEC ta gano sunayen bakin haure a masu rijistan zabe

Hukumar INEC ta gano sunayen bakin haure a masu rijistan zabe

Shugaban INEC din ya ce hukumar zata ci gaba da hada kai da dukkanin hukumomin tsaro domin dakile duk wani rijista da baya bisa doka.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Zamfara ta nada Dan Ali a matsayin sabon sarkin Birnin Magaji

Ya kuma jaddada cewa hukumar zata magance duk wani kalubale da take fuskant, sannan cewa zata mallakawa duk wadanda sukayi rijista katinsu na din-din-din kfin zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel