Nigerian news All categories All tags
Motoci makare da takin noma sun sha bata a gwamnatin baya - Buhari

Motoci makare da takin noma sun sha bata a gwamnatin baya - Buhari

- Shugaba Muhammadu Buhari ya yi shagude ga gwamnatocin da suka shude a Najeriya

- Shuagaban ya bayyan a cewa akasin yadda ya faru a gwamnatocin baya, motocci 3,333 makare da takin zamani sun dauko takin ba tare da ko guda ya bace ba

- Shugaba Buhari ya yi wannan furucin ne yayin da yake ganawa da mambobin Kwamitin samar da taki na musamman a Abuja

A yau Juma'a ne shugaba Muhammadu Buhari ya sake yin shagude ga gwamnatocin baya kan yadda motoci makera da takin zamani suka bace a hanya kafin su kai ga manoma da ya kamata suyi amfani dashi.

Buhari ya yi wannan furucin ne lokacin da ya ke gana wa da mambobin kwamitin shugaban kasa na musamman kan samar da takin noma a fadar Aso Villa da ke Abuja.

Buhari ya yi shagude ga gwamnatocin baya game da batar takin zamani

Buhari ya yi shagude ga gwamnatocin baya game da batar takin zamani

Ya bayyana farin cikin sa bisa yadda dukkan motoci 3,333 da suka dauko taki karkashin shirin na kwamitin na sa suka isar da takin ba tare da an samu ko guda ta bace ba akasin yadda abubuwa suka rika faruwa a gwamnatocin baya.

KU KARANTA: Gwamnati ta fadada neman 'yan matan Dapchi zuwa kasashen Chadi, Nijar da Kamaru

Shugaban ya yi alkawarin cewa gwamnatin sa za ta cigaba da samar da tsaro don ganin shirin ya cigaba.

Bayan mika godiyar sa da babban Bankin Kasa CBN, Ministan Noma da Raya karkara da kuma gwamnonin jihohi, shugaban kasan ya kuma bukace su da su cigaba da aiki tukuru kamar yadda suka fara.

Ya kuma shawarci sauran maso ruwa da tsaki da su cigaba da bawa shirin goyon baya saboda Najeriya tayi ban kwana da siyo taki daga kasashen waje.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel