Nigerian news All categories All tags
An dakatar da ma'aikatan lafiya 4 da laifin bude kwakwalwar wani mara lafiya bisa kuskure

An dakatar da ma'aikatan lafiya 4 da laifin bude kwakwalwar wani mara lafiya bisa kuskure

Wani likitan kwakwalwa ya gamu da bacin rana yayin da aka dakatar da shi sakamakon bude kwakwalwar wani marar lafiya a bisa kuskure da lamarin ya janyo cece-kuce da abin kunya a babban asibitin Kenyatta na kasar Kenya.

Wannan bacin rana ya afku ne yayin da aka shigar da marar sa lafiya biyun a sheme da kowanen su ke fama da ciwo a cikin kawunan su.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, daya daga cikin marar sa lafiya yana fama ne da wata 'yar buguwa cikin ka, yayin da dayan ke fama da taruwar gudan jini a cikin kwakwalwar sa da ya bukaci tiyata domin a debe shi.

An dakatar da ma'aikatan lafiya 4 da laifin bude kwakwalwar wani mara lafiya bisa kuskure

An dakatar da ma'aikatan lafiya 4 da laifin bude kwakwalwar wani mara lafiya bisa kuskure

Sai dai tsautsayi da baya wuce ranar sa ya afku yayin da likitoci suka bude kwakwalwar wanda ba ya da bukatar tiyata, inda sai bayan tsawon awanni cikin tsakiyar aiki suka fahimci kuskuren su na bude kwakwalwar wanda bai cancanta ba.

KARANTA KUMA: Wani 'Dan Majalisar Wakilai ya bayyana inda 'yan Matan Dapchi suke

Shugabar wannan asibiti, Lily Koros, ita ta bayar da wannan rahoto tare da sanarwa ta dakatar da makiwatan lafiya hudu da suke bakin aikin su a ranar da wannan tsautsayi ya afku.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya fayyace sirrin wani tuggu da suka kulla shearu 43 baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel