Nigerian news All categories All tags
Yan matan Dapchi: Yan Boko Haram sun tuntube ni - Aisha Wakil

Yan matan Dapchi: Yan Boko Haram sun tuntube ni - Aisha Wakil

Hajiya Aisha Wakil wacce akafi sani da “Mama Boko Haram”, ta ce yan Boko Haram din da suka sace yan matan Chibok sun tuntubeta.

A wani hira da NAN, Aisha Wakil ta ce bangaren Abu Mus’ab Albarnawi sun tuntubeta kuma sun bayyana mata cewa yan matan na hannunsu.

Tace: “Sune suka kira ni, kuma sun bayyana mini cewa sun ji abinda kuka fada kuma sunce zasu saki yan matan.

“Na rokesu cewa kada wannan ya zama wani kwanaki 1000 na yan matan Chibok, sai sukayi murmushi suka ce A’a.”

“Na tambayesu inda zan iya zuwa domin ganawa da yan matan cikin kwanaki biyu, amma basu ce komai ba.”

“Ina tabbatarwa yan Najeriya cewa sun tare da yarona Habib da abokansa; Habib yarone mai kiri, ba zasu taba su ba, kuma ba zasu kashesu ba.”

Yan matan Dapchi: Yan Boko Haram sun tuntube ni - Aisha Wakil

Yan matan Dapchi: Yan Boko Haram sun tuntube ni - Aisha Wakil

“Zai sauraremu, kuma ya nuna cewa yana son zaman lafiya. Ko shakka babu zasu bamu yan matan. Ina kira ga yan Najeriya da su kwantar da hankulan kuma mu cika da addu’a.”

KU KARANTA: Wata 'Yar Kunar Bakin Wake Ta tayar da Bam a Masallacin Buni-Yadi

Ta yi wannan magana ne bayan gwamnatin tarayya ta ce suna neman yan matan a wasu kasashen da ke makwabtaka da Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel