Nigerian news All categories All tags
Mutane 4 sun mutu a sabuwar rikicin da ta barke a Mambilla

Mutane 4 sun mutu a sabuwar rikicin da ta barke a Mambilla

- Mutane hudu sun rasa rayyukansu a wani sabin rikici da ya barke a tsibirin Mambilla

- Rikicin ya kaure ne tsakanin Fulani da kuma Mazauna yankin na Mambilla

- Wannan dai ba shine karo na farko da irin wannan rikice-rikicen ke faruwa a yankin ba

Mun sami rahoto daga jaridar Thisday da ke nuna cewa sabuwar rikici ya kaure tsakanin mazauna tsibirin na Mambilla da kuma makiyaya a ranar Alhamis 1 ga watan Maris kuma har ya yi sanadiyar rasuwar mutane hudu.

A cewar rahoton, an fara jayaya kan wata fili ne da ke Nguroje sannan abin ya watsu zuwa Jakarta. Rikicin ya yi sanadiyar kone-konen gidaje da dukiyoyi masu yawa daga bangarorin biyu.

Mutane 4 sun mutu a sabuwar rikicin da ta barke a Mambilla

Mutane 4 sun mutu a sabuwar rikicin da ta barke a Mambilla

KU KARANTA: Buri na shine zuwa makarantar boko don in zama malami a garin mu, inji wani almajiri dan shekara

Rikicin ya faru ne duk da cewa hukumar Sojin Najeriya ta kaddamar ta atsayen 'Ayema Akpatuma' a yankin da ya hada da jihar ta Taraba da rikicin ya faru. Sai dai a halin yanzu, jami'an tsaro sun garzaya garin don kwantar da tarzomar.

Duk kokarin da akayi don ji ta bakin rundunar yan sandan na jihar ko kuma shugaban karamar hukumar duk sun ci tura.

A gefe guda, Rundunar Yan sanda reshen Jihar Taraba ta dauki alkawarin hukunta duk wanda aka samu yana karya dokar hana kiwo a fili da gwamnatin jihar ta kafa.

An kafa dokar ne shekarar 2017 amma an kaddamar da ita a ranar Talata 24 ga watan Janairun 2018 duk da cewa wasu al'umma da yawa basu amince da hakan ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel