Nigerian news All categories All tags
Hukumar EFCC ta kwato N750bn cikin shekaru 2 - Femi Falana

Hukumar EFCC ta kwato N750bn cikin shekaru 2 - Femi Falana

Lauya, Mr Femi Falana a ranan Laraba ya bayyanawa kungiyar yan kwadagon Najeriya cewa hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta kwato kudi biliyan N750 cikin shekaru biyun da suka gabata.

Falana, wanda yayi jawabi a taron cikan kungiyar NLC shekaru 40 a garin Abuja ya kalubalanci kungiyar ta san abinda gwamnati ke shirin yi da kudaden.

Yace: “Hukumar EFCC ta kwato N750 billion cikin shekaru 2. Wajibi ne NLC ta binciko abinda zamuyi da kudaden nan.”

Hukumar NLC na rawan takawa domin kare mutuncin mutanen Najeriya. Shi yasa duk lokacin aka samu matsala a kasa, mutane zasu dinga tambaya ina NLC.

Hukumar EFCC ta kwato N750bn cikin shekaru 2 - Femi Falana

Hukumar EFCC ta kwato N750bn cikin shekaru 2 - Femi Falana

“Na fadawa gwamnati cewa yaki da cin hanci da rashawan da suka je suna yaka somintabi ne kawai, basu fara ainihin yakin ba.”

“Na rubuta wasika ga ministan kudi kuma na zayyana mata yadda kasarnan zata gano kudi dala biliyan 200 saboda haka, ba sai an je neman bashi ko ina ba. Amma har yau minista bata gama duba wasikar ba.”

“A shekaran 200, tsohon gwamnan babban bankin tarayya, Chukuma Soludo ya baiwa bankuna kudi dala biliyan 7 amma basu biya ba har yanzu. Hakazalika tsohon gwamna Sunusi Lamido ya baiwa bankuna 6 kudi dala biliyan 600 amma har yanzu basu biya ba.

KU KARANTA: An damke fasto mai ajiye bindigogi a cocinsa

“Zaku tuna cewa an bada miliyan 100 domin farfado fa masaka, amma har yanzu ba’ayi ba. Ina kudaden suka shiga? “

“Shirya nike da baiwa hukumar NLC takardu saboda su amfani wajen cinikin sabon kudin makamai.”

Mr Falana yace babu bukatan Najeriya ta tafi amsa bashi a kasar Sin saboda tanada isassshen kudi a hannu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel