Nigerian news All categories All tags
Dalilan da ya sa ban hallarci tarrukan APC ba - Saraki

Dalilan da ya sa ban hallarci tarrukan APC ba - Saraki

- Kakakin Majalisar Dattawa, Dr Bukola Saraki ya bayyana dalilan da ya sa bai samu hallartan muhimman tarunka jam'iyyar APC da aka gudanar ba

- Sarakin bai hallarci taron Manyan APC na kasa da aka yi ranar 27 ga watan Fabrairu da kuma taron Kwamitin masu gudanarwa na APC da akayi a ranar 27 ga watan Fabrairu

- Kamar yadda hadimin Kakakin majalisar ya sanar, Sarakin ya yi balaguro ne kana ya kuma tafi kotun da'ar ma'aikata inda ya ke cigaba da amsa tambayoyi

Rashin hallartan taron APC guda biyu da kakakin majalisar dattawa Bukola Saraki bai yi ba a makon da ya wuce ya janyo wasu na hasashen cewan yana da niyyar barin jam'iyyar ne shi yasa ya fara janye jiki.

Daliln da ya sa ban sami hallartan taron APC ba - Saraki

Daliln da ya sa ban sami hallartan taron APC ba - Saraki

Sai dai Saraki ya karyata wadanan jita-jita inda ya bayyana cewa bai samu hallartan tarukan bane don ya ci karo da ranar sauraron tuhumar da ake masa a kotun da'ar ma'aikata da kuma wani balaguro da ya yi don hallartan wani taro a jihar Edo.

KU KARANTA: NAHCON ta gargadi maniyyata su kasance masu biyaya ga doka yayin aikin hajji

Cikin sakon da mai magana da yawun Saraki, Alhaji Yusuf Olaniyonu ya aike wa Legit.ng, ya bayyana cewa Saraki ya hallarci taron na musamman kan safarar mutane a garin Benin na jihar Edo wanda yana daya daga cikin matakan da majalisar ta dauka don magance matsalar kuma bai dawo Abuja ba kan lokaci.

A ranar Talata da aka gudanar da taron NEC na jam'iyyar APC, Sarakin ya hallarci sauraron karar sa da ake gudanar wa a kotun da'ar ma'aikata don ya wanke kansa daga zargin da ake masa.

Olaniyonu ya gargadi masu yadda jita-jita da manufa mara kyau su guji yin hakan don babu wata dalili na musamman da ya sa Saraki bai hallarci tarukan ba face aiki da kuma shari'ar na sa da ya hallarta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel