Nigerian news All categories All tags
Fashin bankin a jihar Imo: An damke fasto mai ajiye bindigogi a cocinsa

Fashin bankin a jihar Imo: An damke fasto mai ajiye bindigogi a cocinsa

Yan sandan hukumar SARS na jihar Imo sun damke shugaban cocin Jesus The Rock of Salvation Healing Ministry, Uratta, a karamar hukumar Owerri na Arewa, Fasto Chiedozie Anochima, da hannu cikin fashin ranan 22 ga watan Fabrairu, 2017, da akayi a banki.

Harin da aka kai bankin Zenith da ke titin Wetheral Road na garin Owerri a jihar inda aka hallaka yan sanda 2, da kuma jikkata wani dansanda.

Hukumar yan sandan jihar sun samu nasaran damke yan fashin daga baya amma ranan Lahadin da ya gabata ne suke damke fasto a cocinsa.

Wani majiya a hukumar yan sanda ya bayyana cewa damke mamban kungoyar yan fashi, Chinonso Onwugbuchlam, ne ya basu daman damke faston.

Fashin bankin a jihar Imo: An damke fasto mai ajiye bindigogi a cocinsa

Fashin bankin a jihar Imo: An damke fasto mai ajiye bindigogi a cocinsa

Chinonso Onwugbuchlam, ya ambaci sunan faston ne yayin bincike da jami’an SARS din ke gudanar da bincike akansa.

KU KARANTA: Gobara ta lashe sama da shaguna 600 a kasuwar Bida

Yace: “Chinonso Onwugbuchlam ya ambaci wani fasto mai suna, Fasto Chiedozie Anochima a matsayin abokin aikinsu. Faston mai shekaru 36 da haihuwa wanda ya assasa cocin Jesus The Rock of Salvation Healing Ministry, da ke Urratta, karamar hukumar Owerri, jihar Imo.”

Ya kara da cewa faston ne ke ajiye musu makamai kuma ke taimaka musu da addu’a inda zasu je fashi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel