Nigerian news All categories All tags
Majalisar wakilai tana tuhumar kamfanoni 31 bisa zargin su da cin hanci da rashawa

Majalisar wakilai tana tuhumar kamfanoni 31 bisa zargin su da cin hanci da rashawa

- Majalisar wakilai tana tuhumar wasu kamfanoni da almundahana

- Kwamitin tace kamfanonin sun saka Najeriya gagarumar asara

- Kamfanonin suna fitar da kaya ba bisa ka'ida ba

Majalisar wakilai tana tuhumar kamfanoni 31 bisa zargin su da cin hanci da rashawa

Majalisar wakilai tana tuhumar kamfanoni 31 bisa zargin su da cin hanci da rashawa

Majalisar wakilai ta kasa ta fara gudanar da wani bincike akan wasu kamfanoni bisa zargin su da sayar da kaya ba bisa ka'ida ba. Kwamitin kwastam, wanda dan majalisar jiha Abiodun Faleke (APC, Lagos) ya ke wakilta, ta yanke shawarar ta kira dukkan kamfanonin da ke da hannu domin warware batun.

DUBA WANNAN: An kama faston karya a jihar Imo yana neman yaudarar mutanen shi

Kwamitin ta ce kayan da aka fitar dasu din sun saka Najeriya gagarumar asara, inda ta rasa biliyoyin nairori, saboda rashin bin doka.

Kamfanonin da ake tuhuma sun hada da Mac Resolute Services Ltd; Viscous Global Investment; Fadobra Ventures Ltd; China Homes and Office Equipment; Links World Redemption Enterprises; Seaview Emporium Ltd; Pancham International Ltd; Alfatek Integrated Ventures; Verona Industries Ltd; Vital Products Ltd da kuma Odun & Remy Trading Company.

Sannan kuma akwai SCC Nigeria Limited; J.I. Ejison International Nigeria Limited; Tak Continental Ltd; Metal African Steel Products; Sunshine Guest House & Hotel; Elim Top Suite Ltd; Noktel Resort Hotel; Naks Hotels & Tower Ltd; Luxurium Leisure Service; Chelsea Hotel and Vinimo.

Da yake jawabi a birnin Abuja, Faleke ya ce kwamitin ta kaddamar da binciken da ya dace, tare da cewa akwai "zargin cin hanci da rashawa ta ta hanyar shigar da kayyaki da ke haifar da asarar kudaden shiga a kasar nan.

Ya ce: "rashin bin doka da kuma cin hanci da rashawa da wasu kamfanoni ke yi ya saka kasar nan asarar kudade sosai, ya ce ba wai ana zancen biliyan bane ana zancen tiriliyan ne abinda kasar ta yi asara.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel