Da dumi-dumi: Hankalin al’umma ya tashi yayinda yan Boko Haram suka kai kar garin Rann

Da dumi-dumi: Hankalin al’umma ya tashi yayinda yan Boko Haram suka kai kar garin Rann

Da alamun anyi asaran rayuka a daren jiya Alhamis yayinda Boko Haram ta kai hari kauyen Rann, Shelkwatan karamar hukumar Balge na jihar Borno.

Idanuwan shaida a kauyen sunce sun zaune kalau sai yan Boko Haram sun kawo musu hari ba zato.

Wani sakon rediyo da wata mata mai aiki da wani kungiyar agaji ta turo ya tabbatar da aukuwan wannan hari.

Babu na’urar wayan tarho a garin Rann, amma masu bayar da agaji na amfani da na’urar ‘Wifi’ domin tattaunawa da abokansu.

Da dumi-dumi: Hankali al’umma ya tashi yayinda yan Boko Haram suka kai kar garin Rann

Da dumi-dumi: Hankali al’umma ya tashi yayinda yan Boko Haram suka kai kar garin Rann

Matan ta tattauna da abokinta misalin karfe 8 zuwa 9 na dare. A sakon ta, ta sanar da abokin cewa an kawo musu hari amma sun samu tserewa barikin soji.

KU KARANTA: Gobara ta lashe sama da shaguna 600 a kasuwar Bida

Muryanta na karshe da aka ji shine lokacin da yan Boko Haram din suka afka barikin sojin kuma sun yiwo kansu.

Ta ce: “ Wayyo Allah ga su nan sun shigowa, zasu kashe ni….”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel