An kama faston karya a jihar Imo yana neman yaudarar mutanen shi

An kama faston karya a jihar Imo yana neman yaudarar mutanen shi

- Hukumar 'yan sanda ta kama wani faston bogi a jihar Imo

- Ta kama shi da hada kai da wasu mutane da nufin sace wata yarinya domin ya damfari mutanen shi

- Bayan haka hukumar ta kama shi da laifin karya da yaudarar mutanen cocin nashi

An kama faston karya a jihar Imo yana neman yaudarar mutanen shi

An kama faston karya a jihar Imo yana neman yaudarar mutanen shi

Hukumar ‘yan sanda ta kama wani fasto mai suna Benjamin Ndieze, wanda ke shugabantar cocin Home of Deliverance Assembly, Ihiagwa garin Owerri Jihar Imo, inda ya shirya da wata mata mai suna Blessing Ahamefula dake unguwar Ihie Orji Umuonyaogu Ngwa Road, Aba a jihar Abia da tazo cocin sa a Ihiagwa da ‘yarta mai suna Faith Ahamefula, ‘yar shekaru 5 a ranar 30/01/2018.

DUBA WANNAN: Badakalar mai: Omokore ya bawa Secondus da Adamu Mu'azu motoci 33

Matar ta je cocin ta ba wa Faston yarinyar inda shi kuma yaba wa wani daga cikin ‘yan cocin, mai suna Emmanuel Onuoha, ya kuma umurce shi da ya kai yarinyar ya ajiyeta gidan mai na NNPC a Control post, a garin Owerri.

A lokacin da suka taru a cocin domin bauta, sai fasto ya fadi cewa akwai wata mata a cikin mutanen da ke cikin cocin nan wadda ta ke neman 'yarta wadda kawunta mai suna Emeka, ya sace daga garin Aba, an kai yarinyar garin Onitsha daga nan za’a tafi da ita garin port-harcourt, jihar Rivers.

Faston yace zai yi addu’a, kuma karfin addu'ar tasa zata saka duk wadan da suka sace ta zasu aje ta a NNPC control post, na garin Owerri; ya kuma ce duk wanda ke son yaga mu'ujiza da kuma karfin addu'arsa to ya biyo shi suje NNPC Control Post, a Owerri don su gani da idonsu.

Zuwan su wurin shine ya dakko hankalin hukumar 'yan sanda, suka zo suka yi gaba dashi

Bayan da hukumar ‘yan sanda tayi bincike ta gano cewar faston bogi ne sannan ta gano cewa banda wannan ma ya damfari dayawa daga cikin mutanen cocin ta hanyar basu labaran karya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel