Gowon cike da mamaki: Obasanjo ya bayyana wani Sirri kan tsohuwar gwamnatin su shekaru 43 baya

Gowon cike da mamaki: Obasanjo ya bayyana wani Sirri kan tsohuwar gwamnatin su shekaru 43 baya

A yayin bikin kaddamar da littafi na tarihin rayuwar tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Dakta Ahmadu Ali, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya fayyace sirrin wani tuggu da suka kulla a lokacin tsohuwar gwamnati ta mulkin Soja, Janar Yakubu Gowon.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne aka gudanar da wannan biki a dakin taro na Yar'Adua Centre dake babban birni na tarayya, wanda Obasanjo ya kasance shugaban taro da kuma Gowon a matsayin Uban taro.

Legit.ng ta fahimci cewa, cikin raha da annashuwa tsaffin shugabannin uku sun tuna tarihi tare da tunatar da juna da kuma mahalarta bikin wasu sirrika na rayuwar su da suka shude shekaru aru-aru.

A yayin haka ne Obasanjo ya bayar da wani tarihi na ranar da aka haife da ta kasance ranar cin Kasuwar kauyen su, da ya sanya daukacin mahalarta taron cikin kyalkyala.

Janar Yakubu Gowon

Janar Yakubu Gowon

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, Obasanjo ya kuma bayyana wani tuggu da suka tare da tsohon shugaban jam'iyyar Ahmadu Ali, inda suka kulla tuggu na korar wasu ma'aikatan kasar Amurka daga ma'aikatar su ta jihar Legas da ya janyo cece-kuce da kunyata Najeriya a idon duniya.

KARANTA KUMA: Dalilin da yasa Shugaba Buhari zai amince da sauya Kundin Tsari - Dogara, Saraki

A wannan shekara ta 1975, Janar Gowon shine jagoran kasar nan da lamarin ya sanya ya kausasa harshe kan Obasanjo, wanda hakan bai sanya ya tona asirin Ahmadu ba sai bayan shekaru 43 da suka shude.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a ranar ta gabata ne dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi sabbin jakadu 3 na kasashen ketare a fadar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel