Badakalar mai: Omokore ya bawa Secondus da Adamu Mu'azu motoci 33

Badakalar mai: Omokore ya bawa Secondus da Adamu Mu'azu motoci 33

- An rabawa tsohon shugaban jam'iyyar PDP da shugaban jam'iyyar na yanzu motoci 33

- An bawa Adamu Mu'azu motoci 23 na alfarma, inda shi kuma Uche Secondus ya samu guda 10

- Ana tuhumar Omokore da badakalar kudi kimanin dalar Amurka biliyan 1

Badakalar mai: Omokore ya bawa Secondus da Adamu Mu'azu motoci 33

Badakalar mai: Omokore ya bawa Secondus da Adamu Mu'azu motoci 33

Wani shaida ya bayyana yadda Jide Omokore, ya rabawa shugaban jam’iyyar PDP na yanxu, Uche Secondus da tsohon shugaban jami’iyyar ta PDP Adamu Mu’azu, motoci a wata Yulin shekarar 2014.

Olawale Oloyede, ma'aikacin kamfanin Skymit Ltd, ya shaidawa babbar kotun tarayya a Abuja cewa, an bawa Adamu Mu’azu motoci 23 shi kuma Secondus an bashi guda 10.

DUBA WANNAN: Dakarun Najeriya sun tarwatsa sansanin 'yan boko haram, sannan sun kashe mutum biyar

Wani ma'aikacin hukumar EFCC, Rotimi Jacobs, ya bayyana cewa, Oloyede, ya fadi yanda Omokore, ya bada umurnin rabawa mutanen motocin, inda ya ce a bawa Mu’azu Hilux 2, Landcruiser 5, Camry 2, Honda 3, Avalon 4, Lexus G460 da Lexus LX570, Benz S550 da kuma E200.

Bayan da shi ya dauki motoci masu sulke wand kudaden su zai kai miliyan 35 zuwa 70, sannan ya raba wa mutane da yawa kyautar motocin ciki harda kungiyoyi da kuma kamfanoni wanda darajar su ta kai ta miliyan 9 zuwa 70 kowace.

A binciken da masu kare shi suka yi sun ce wasu daga cikin motocin an saye su akan bashi ne, sun kara da cewa, shi din kuma bai sani ba ko a matsayin cin hanci aka bada motocin.

Hukumar ta EFCC ta zargi, Omokore, wanda yake Manajan Darekta na Atlantic Energy Ltd, da zargin cin kudin gwamnatin tarayya kimanin dalar Amurka Biliya 1.

Kotu za ta cigaba da sauraron karar ranar Juma’a.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel