Nigerian news All categories All tags
Dakarun Najeriya sun tarwatsa sansanin 'yan boko haram, sannan sun kashe mutum biyar

Dakarun Najeriya sun tarwatsa sansanin 'yan boko haram, sannan sun kashe mutum biyar

- Rundunar sojin Najeriya sun yi fata-fata da sansanin 'yan boko haram

- Sun kashe mutum biyar daga cikin 'yan tawayen

- Biyu daga cikin sojojin sun rasa rayukan su sakamakon raunukan da suka samu yayin harin

Dakarun Najeriya sun tarwatsa sansanin 'yan boko haram, sannan sun kashe mutum biyar

Dakarun Najeriya sun tarwatsa sansanin 'yan boko haram, sannan sun kashe mutum biyar

Rundunar Sojin Operation Lafiya Dole sun kaiwa 'yan kungiyar Boko Haram hari a cikin dajin Sambisa, inda suka samu nasarar tarwatsa sansanin su, tare da kashe biyar daga cikin su; sai dai kuma anyi asarar mutum biyu daga cikin sojojin dalilin raunukan da suka samu yayin kai harin.

DUBA WANNAN: Wani matashi ya budewa motar Sarauniyar Ingila wuta

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar sojin Col. Onyema Uwachukwu, ya yi a wani taro a garin Maiduguri, ya ce dakarun rundunar Operation Deep Punch, sune suka koro 'yan kungiyar boko haram din daga cikin dajin Sambisa.

"Rundunar ta samu nasarar ta samu nasarar lalata sansanin su dake Agapulawa, Amuda, Nyawa da kuma Attagara; duk a cikin wani bangare na dajin Sambisa," inji shi. Sannan ya bayyana cewa dakarun sun cigaba da kutsawa dajin domin tarwatsa sauran sansanin 'yan ta'addan da aka gano a kusa da Tchikide da Chinene.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel