Nigerian news All categories All tags
Sauya sheka: Hadimin Bukola Saraki yayi karin haske game da barin APC zuwa PDP

Sauya sheka: Hadimin Bukola Saraki yayi karin haske game da barin APC zuwa PDP

Biyo bayan kin halartar manyan tarukan jam'iyyar APC mai mulki da shugaban majalisar dattijan Najeriya, Sanata Bukola Saraki yayi a farkon makon nan, kishin-kishin ta yawaita na cewar ko yana shirin ficewa daga jam'iyyar ne zuwa jam'iyyar sa ta PDP.

To sai dai wani babban hadimin sa mai taimaka masa ta fuskar yada labarai Mista Yusuph Olaniyonu ya bayyana cewa wadannan zarge-zargen ba gaskiya ba ne domin shi Saraki din ba ya tsoron kowa.

Sauya sheka: Hadimin Bukola Saraki yayi karin haske game da barin APC zuwa PDP

Sauya sheka: Hadimin Bukola Saraki yayi karin haske game da barin APC zuwa PDP

KU KARANTA: Sanata Melaye ya samu belin Naira dubu 100

Legit.ng ta samu cewa a cikin sakon da Mista Yusuph din ya fitar ya kuma rabawa manema labarai, ya bayyana cewa uban gidan sa ba matsoraci bane da zai sulale ta taga idan zai bar jam'iyya, ya bayyana cewa idan yana so ya fita zai fita ne ta kofa domin kowa ya sani kamar yadda yayi a baya.

A wani labarin kuma, Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake da alhakin gudanar da zabuka ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC) ta ayyana cewa yanzu haka kungiyoyi 108 ne ke neman rijista a matsayin jam'iyyu kafin zaben 2019.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakub shine ya sanar da hakan a jiya Alhamis a yayin jawabin sa a wajen wani taro da yanzu haka ke cigaba da gudana na dandalin sada zumunta na mako daya watau 'Social Media Week'.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel