Nigerian news All categories All tags
Abun kunya: Najeriya ce kadai kasar da ke da arzikin mai amma take shigowa da shi - NNPC

Abun kunya: Najeriya ce kadai kasar da ke da arzikin mai amma take shigowa da shi - NNPC

Kasar Najeriya kawo yanzu ita kadai cewa mamba a jerin kasashe masu arzikin man fetur na duniya na kungiyar Organisation of Petroleum Exporting Countries (OPEC) a turance dake shigowa da man da take anfani da shi.

Wannan dai na kunshe ne a cikin jawabin shugaban rukunin kamfunnan albarkatun man fetur na kasa wata National Petroleum Corporation (NNPC), Dr. Maikanti Baru da yayi a garin Abuja, yayin wani taron masu ruwa da tsaki a harkan man fetur din da daya daga cikin manyan ma'aikatan hukumar Alhaji Bello Rabi'u ya wakilta.

Abun kunya: Najeriya ce kadai kasar da ke da arzikin mai amma take shigowa da shi - NNPC

Abun kunya: Najeriya ce kadai kasar da ke da arzikin mai amma take shigowa da shi - NNPC

KU KARANTA: Saurayi mai neman matan aure ya shiga hannu

Haka ma kuma shugaban na NNPC ya kara da cewa kasar ta Najeriya kawo yanzu ta fi kowace kasa a duniya shigo da man fetur din daga kasashen waje wannan kuma a cewar sa wannan abun kunya ne da ya kamata a gyara.

A wani labarin kuma, Kungiyar nan ta addinin Islama ta Jama’atu Nasril Islam karkashin jagorancin Sarkin musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar na III a jiya Alhamis sun yi tofin Allah tsine ga gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari game da satar 'yan matan makarantar Dapchi 110.

Kungiyar dai ta bayyana cewa wannan sakacin na gwamnati abun takaici ne kuma ya kawo koma baya ga ilimin 'ya'ya mata a yankin na Arewacin Najeriya wanda kuma hakan ba karamin nakasu bane ga yankin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel