Dapchi: Sultan, Jama’atu Nasril Islam sun yi tofin Allah-tsine ga shugaba Buhari

Dapchi: Sultan, Jama’atu Nasril Islam sun yi tofin Allah-tsine ga shugaba Buhari

Kungiyar nan ta addinin Islama ta Jama’atu Nasril Islam karkashin jagorancin Sarkin musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar na III a jiya Alhamis sun yi tofin Allah tsine ga gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari game da satar 'yan matan makarantar Dapchi 110.

Kungiyar dai ta bayyana cewa wannan sakacin na gwamnati abun takaici ne kuma ya kawo koma baya ga ilimin 'ya'ya mata a yankin na Arewacin Najeriya wanda kuma hakan ba karamin nakasu bane ga yankin.

Dapchi: Sultan, Jama’atu Nasril Islam sun yi tofin Allah-tsine ga shugaba Buhari

Dapchi: Sultan, Jama’atu Nasril Islam sun yi tofin Allah-tsine ga shugaba Buhari

KU KARANTA: Kusoshin PDP da APC za su yi wa Buhari taron dangi a 2019

Legit.ng dai ta samu cewa wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban Sakataren kungiyar Dakta Abubakar Khalid Aliyu ya sanya wa hannu ya kuma rabawa manema labarai a garin Kaduna inda ya bayyana cewa kamata yayi ace kawo yanzu gwamnati ta dauki kwakkwaran mataki ga wadan da suka yi sakacin.

A wani labarin kuma, Kasar Najeriya kawo yanzu ita kadai cewa mamba a jerin kasashe masu arzikin man fetur na duniya na kungiyar Organisation of Petroleum Exporting Countries (OPEC) a turance dake shigowa da man da take anfani da shi.

Wannan dai na kunshe ne a cikin jawabin shugaban rukunin kamfunnan albarkatun man fetur na kasa wata National Petroleum Corporation (NNPC), Dr. Maikanti Baru da yayi a garin Abuja, yayin wani taron masu ruwa da tsaki a harkan man fetur din da daya daga cikin manyan ma'aikatan hukumar Alhaji Bello Rabi'u ya wakilta.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel