Nigerian news All categories All tags
NAHCON ta gargadi maniyyata su kasance masu biyaya ga doka yayin aikin hajji

NAHCON ta gargadi maniyyata su kasance masu biyaya ga doka yayin aikin hajji

- An shirya wani taron fadakarwa na kwana daya don wayar da kan maniyattan jihar Katsina

- An shawarce maniyattan suyi biyaya ga dokokin kasar ta Saudiyya domin kaucewa fadawa cikin matsala

- An gargadi maniyatan cewa mahukuntar kasar Saudiyya basu lamuntar laifi ko da cikin rashin sani aka aikata shi

An gargadi maniyyatan aikin hajji daga jihar Katsina su kasance masu bin doka da oda a lokacin da suka isa kasa mai tsarki don mahukuntar kasar ba za bata lokaci ba wajen hukunta duk wanda aka samu yana aikata laifi.

A jawabin da ya yi wajen taron fadakarwa na kwana daya da aka shirya a jihar, Jami'in hukumar aikin hajji na kasa, Dr. Aliyu Tanko ya bayyana cewa akwai mutane da dama da ke kurkuku a kasar Saudiyya saboda sun aikata laifi bisa rashin sani.

NAHCON ta gargadi maniyyata su kasance masu biyaya ga doka yayin aikin hajji

NAHCON ta gargadi maniyyata su kasance masu biyaya ga doka yayin aikin hajji

A cewar sa, a bara an gano da na'urar kyamarar CCTV inda wani maniyyaci da tsinta wani abu a kasa amma a maimakon ya jawo hankalin Yan sanda sai ya dauka da kansa, hakan yasa mahunkar kasar suke garkame shi a kurkuku.

KU KARANTA: Gobara ta lashe sama da shaguna 600 a kasuwar Bida

Tanko ya kuma shawarci maniyattan su rika tafiya cikin tawaga don jami'an NAHCON su rika samun saukin gane su idan suna neman su.

A nasa jawabin, babban direktan hukumar maniyata, Abu Rimi ya ce an shirya taron bitar ne don a wayar da kan maniyyatan kan sabbin dokokin da kasar ta Saudiyya ta kafa.

Ya kuma bukaci maniyyatan su mayar da hankali wajen saurarar fadakarwar da za'a yi musu don gudun fadawa cikin matsala.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel