Nigerian news All categories All tags
2019: Jiga-jigan APC da PDP za su sauya shekar siyasa yau a cikin dare

2019: Jiga-jigan APC da PDP za su sauya shekar siyasa yau a cikin dare

- Manyan a Jam’iyyar APC da PDP na daf da sauya shekar siyasa

- A yau dinnan wasu jiga-jigan Jam’iyyun za su koma jirgin SDP

- Na cikin gidan APC da PDP za su hadu su ba APC kashi a 2019

Wani babban labari ya zo mana ba da dadewa ba Daga Daily Independence cewa wasu manya cikin gidan Jam’iyyar APC da kuma PDP za su hadu su koma Jam’iyyar SDP domin su kada Shugaba Buhari.

2019: Jiga-jigan APC da PDP za su sauya shekar siyasa yau a cikin dare

‘Yan APC da PDP za su hadu su ba Shugaba Buhari kashi

Jiga-jigan manyan Jam’iyyu 2 na kasar za su sauya sheka ne zuwa Jam’iyyar SDP ta su Olu Falae a daren nan. Shugaban Jam’iyyar ta SDP Cif Olu Falae ne ya bayyana wannan a jiya Alhamis da dare kamar yadda mu ka ji.

KU KARANTA: Obasanjo ba barazana bane ga Shugaba Buhari - APC

Falae yace manyan ‘Yan siyasa daga sauran Jam’iyyun kasar za su shigo jirgin SDP domin kada Jam’iyyar APC a zabe na gaba. Za ayi amfani da Jam’iyyar SDP ne domin ganin an kauda PDP da APC daga mulkin kasar.

Olu Falae yace wasu ‘Yan Majalisun kasar da tsofaffin Gwamnoni da manyan Jam’iyyun APC da PDP za su shigo Jam’iyyar su ta SDP da karfe 8 na daren yau. Za ayi wannan bikin sauya sheka a dakin taro na Ladi Kwali a Abuja.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel