Rashin isassun dakuna ya jawo annobar sankarau a Jami’ar Dutsin-Ma

Rashin isassun dakuna ya jawo annobar sankarau a Jami’ar Dutsin-Ma

- Cutar sankarau yayi sanadiyyar mutuwar wasu ‘Dalibai 2 a Katsina

- Annobar ta nemi ta shiga Jami’ar Tarayya da ke Garin Dutsin-Ma

- Hukumar Jami’ar ta karyata rade-radin da ke yawo na rashin kula

Mun samu wani rahoto daga Jaridar Daily Trust cewa mutuwar wasu ‘Dalibai 2 kwanan nan ya jefa Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Dutsinma a Jihar Katsina cikin rudu a halin yanzu.

Wani ‘Dalibi da ke karantar harkar lissafi Kayode Aliyu Gabriel da kuma wani Abubakar Safiyanu duk a sasshen na lissafi sun riga mu gidan gaskiya a makonnin da su ka wuce. Aliu ya rasu ne bayan kwana uku Safiyanu ya bi baya.

KU KARANTA: Gwamnonin Arewa na wani muhimmin taro a Jihar Kaduna

Har yanzu dai an rasa gane abin da ya kashe ‘Daliban, sai dai an zargin sankarau ne yayi wa ‘Daliban Makarantar katutu saboda yawan da aka yi a cikin daki a lokacin yanzu da ake fama da mugun zafi musamman a Yankin.

‘Dalibai kan biya kudin da ya haura N10, 000 domin zama a dakin mutum 4 amma ana zama ne da kusan mutane 15 a wasu Dakunan. Jami’ar dai ta karyata wannan inda tace hakan ba gaskiya bane don an haramta cinkoso a dakuna.

Isyaku Yusuf Karofi wanda ke magana da yawun Jami’ar yace daya daga cikin marasa lafiyar bai je asibiti ba ne shiyasa abin ya kai ga haka. Yanzu dai wasu na ta yada cewa ‘dalibai 10 zuwa 20 su ka rasu dalilin wannan annoba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel