Nigerian news All categories All tags
Wani abu guda ɗaya rak da Ganduje ke bukata daga Kwankwaso matukar yana son ayi Sulhu

Wani abu guda ɗaya rak da Ganduje ke bukata daga Kwankwaso matukar yana son ayi Sulhu

Biyo bayan kiraye kiraye da ake ta yi ma bangarorin jiga jigan siyasar Kano da basa ga maciji, bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje da na Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Gwamnan ya gindaya sharadin yin sulhu.

Gwamnan ta bakin kwamishinan watsa labaru, al’amuran matasa da al’adun gargajiya, Kwamared Muhammad Garba ne ya bayyana haka, inda yace gwamna Ganduje ya yi duk abinda za iya a baya don ganin ya sulhunta da Kwankwaso, amma Kwankwaso ya yi watsi da wannan tayi.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari zata sake kashe naira biliyan 16.6 don gudanar da ayyukan titiuna a kudancin kasar nan

Garba ya bayyana haka a wani shirin siyasa na gidan rediyon Freedom fm Kaduna, inda yace sharadin da gwamna Ganduje ya shimfida shi ne, duk wasu yan gaban goshin Kwankwaso da suka dinga furta kalaman batanci ga Ganduje su nemi afuwa, idan kuma ba haka ba, toh haihata haihata!

Garba yace: “Da dama daga cikin yan gaban goshin Kwankwaso sun furta kalaman batanci ga gwamnan jihar Kano da nufin cin zarafinsa da cin mutuncinsa, don haka muddin suna bukatar sulhu da gwamnan, sai sun rubuta takardar neman afuwa, a kai ma gwamnan ya duba ya gani, idan ya amince, sai su sanya hannu, shi kenan.”

Daga cikin sunayen yan gaban goshin tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da kamishina Garba ya ambata, har da Dakta Dangwani, tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Kano, inji rahoton majiyar Legit.ng.

Idan mai karatu bai manta ba, danganta ta yi tsami ne a tsakanin Kwankwaso da Ganduje tun bayan darewar gwamna Ganduje mukamin Gwamna, inda yayi zargin tun kafin a rantsar da shi ya lura Kwankwaso bai son gwamnatinsa ta samu nasara.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel