Nigerian news All categories All tags
Dapchi: Wani Sanata ya nemi Sojojin Najeriya su ji da aikin gaban su

Dapchi: Wani Sanata ya nemi Sojojin Najeriya su ji da aikin gaban su

- Rashin tsayawa ayi aiki ya ja aka sace 'Yan Makaranta a Garin Dapchi

- Sanata Shehu Sani na Jihar Kaduna ya bayyana wannan kwanan nan

- Jami'an Sojoji kan shiga harkokin kasuwanci wanda yace bai dace ba

Sanata Shehu Sani na Kaduna ta tsakiya yayi amfani da shafin sa na sada zumunta na zamani watau Tuwita inda ya bayyana ra'ayin sa game sa sha'anin tsaro a Yankin Arewa maso gabashin kasar Najeriya a cikin makon nan.

Dapchi: Wani Sanata ya nemi Sojojin Najeriya su ji da aikin gaban su

Bai dace Sojoji su rika aikin lura da otel ba - Shehu Sani

Sanatan na Jihar Kaduna yana ganin bai dace ace Sojoji su rika wasu ayyuka irin lura da otel da kafa dakunan biki da shagunan kasuwanci ba domin samun kudi yayin da ake bukatar su a filin daga musamman a Makarantu da sauran su a Yankin.

KU KARANTA: Ihu bayan hari Shugaba Buhari ya ke yi - Oby Eze

Idan ba ku manta ba kwanan nan aka sace 'Yan makaranta sama da 100 a Yobe. An yi hakan ne bayan Rundunar Sojojin ta dauke Jamia'an ta daga Yankin. Sanatan yace yayin da ake bukatar Sojojin, bai kamata su rika wani aiki na dabam ba.

Sojojin Najeriya kan kafa kasuwanci irin na saida kaya da aikin otel wanda Sanatan yana ganin bai dace ba a wannan marra. Sanatan tace ya kamata Sojoji su tsaya ne su ji da aikin gaban su wanda ya hada da kare yaran makaranta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel