Nigerian news All categories All tags
Satar 'Yan mata: Mun ba Buhari shawara tun tuni amma bai dauka ba Inji tsohuwar Minista

Satar 'Yan mata: Mun ba Buhari shawara tun tuni amma bai dauka ba Inji tsohuwar Minista

- Shugabar Bring Back our Girls ta soki Shugaban kasa Buhari

- Oby Ezekwesili tace Shugaban kasar bai dauki shawarar su ba

- Yanzu haka dai Jamia'an tsaro sun koma Yankin Jihar Yobe da aiki

Daya daga cikin Shugabar Kungiyar Bring Back Our Girls watau Madam Oby Ezekwesili ta caccaki Shugaban kasa Muhammadu Buhari game da 'Yan matan da aka sace a wata Makaranta a Garin Dapchi da ke cikin Jihar Yobe.

Satar 'Yan mata: Mun ba Buhari shawara tun tuni amma bai dauka ba Inji tsohuwar Minista

Oby Ezekwesili ta caccaki Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Tsohuwar Ministar ilmi ta kasar a lokacin Shugaba Olusegun Obasanjo tace sun fi shekaru uku su na neman Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo wani shiri da zai inganta tsaro a Makarantun da ke Yankin Arewa maso gabashin kasar.

KU KARANTA: Majalisa tayi tir da wasu Ministocin Najeriya 2

Ezekwesili dai tace Shugaban kasar bai dauki wannan kira na su ba wanda hakan ya sa aka kara sace wasu 'Yan Makarantar kwana sama da 100 a dare guda a Jihar Yobe. Kungiyar tayi ta kara a tsare Makarantu da ke Yobe, Borno da Adamawa.

Sai bayan aukuwar abin ne dai Gwamnatin Shugaban kasar Buhari ta bada umarni cewa Shugaban Hukumar NSCDC masu kare mutanen Gari da sauran manyan jami'an tsaro su koma Yankin da aka yi wannan ta'adi wanda Ministar tace an makaranta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel